Breaking News

Bana ban sha azumi ko daya ba - Buhari

Rashin lafiyar Buhari ta janyo ce-ce-ku-ce a Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce an kammala azumin Ramadan na bana ba tare da ya sha ko daya ba.

Shugaban ya fadi haka ne a yayin da yake ganawa da al'ummar Abuja da suka kai ma sa ziyarar barka da Sallah a fadarsa karkashin jagorancin ministan birnin Tarayya.

A sanarwar da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Femi Adeshina ya fitar, shugaban ya ce: "Ban yi azumin bara ba saboda rashin lafiya, amma a bana na samu cikakkiyar damar yin azumin."


Shugaba Buhari ya shafe watanni yana jinya a Birtaniya a bara, jinyar rashin lafiyar da har ya dawo ba a bayyana ainihin cutar da ke damunsa ba.

Ko a watan Mayun bana, shugaban ya sake komawa Landan domin ganin likitansa bayan ya dawo daga Amurka.

Shugaban wanda ya bayyana aniyar sake neman wa'adin shugabanci na biyu a zaben 2019 ya ce, "ajiye azumi bai wajaba ga musulmin da ke cikin koshin lafiya ba."

Wannan na nufin shugaban ya samu lafiya daga cutar da ya yi fama da ita wacce a baya ta janyo ce-ce-ku-ce a Najeriya inda har wasu suke ganin shugaban ba zai iya shugabancin kasar ba.

A cikin jawabinsa, Buhari ya yi kira ga 'Yan Najeriya su yi aiki don gyara kasar daga matsalolin da ta fada a baya.

"Ba mu da wata kasa da ta wuce Najeriya. Za mu iya hada kai mu ceto ta gaba daya" in ji shi.
Rashin lafiyar Buhari tun farkon shekarar 2017

Buhari zai sake tsayawa takara a zaben 2019.
 •  19 ga watan Jan - Ya tafi Birtaniya domin "hutun jinya"
 •     5 ga watan Fabrairu - ya nemi majalisar dokoki ta kara masa tsawon hutun jinya
 •     10 ga watan Maris - Ya koma gida, amman bai fara aiki nan-da-nan ba
 •     26 ga watan Afrilu - Bai halarci zaman majalisar ministoci ba kuma "yana aiki daga gida"
 •     28 ga watan Afrilu - Bai halarci Sallar Juma'a ba
 •     3 ga watan Mayu - Bai halarci zaman majalisar ministoci ba a karo na uku
 •     5 ga watan Mayu - Ya halarci sallar Juma'a a karon farko cikin mako biyu
 •     7 ga watan Mayu - Ya koma Birtaniya domin jinya
 •     25 ga watan Yuni - Ya aikowa 'yan Najeriya sakon murya
 •     11 ga watan Yuli - Osinbajo ya gana da shi a Landan
 •     23 ga watan Yuli - Ya gana da wasu gwamnoni
 •     26 ga watan Yuli - Ya sake ganawa da wasu karin gwamnoni

    A watan Mayu 2018 Buhari ya sake komawa ganin likita

No comments