Breaking News

Kun san na'urar da za ta iya kare rayukan masunta?

Dadare aka fi kamun kifi kuma guguwar iska tare da ruwa ta fi faruwa a wannan lokaci
Ba za mu iya hana aukuwar bala'i ba ko da aman wutar dutse ne ko girgizar kasa da guguwar iska mai dauke da ruwa da kuma zaftarewar dusar kankara, amma za mu iya amfani da fasaha wajen ankarar da mutane idan za su fuskanci hadari domin tabbatar da tsaron lafiyarsu.

Rana na gab da faduwa a Tafkin Victoria, wanda shi ne tafki mafi girma a Afirka, inda dubban masunta suka shirya shiga cikin ruwa domin kamun kifi a cikin dare.

Yayin da suke shirin tafiya, sun san cewa rayuwarsu na cikin hadari kuma watakila ba za a sake ganin wasu daga cikinsu ba.Tafkin Victoria na da girma sosai kuma ya ratsa ta Uganda da Tanzaniya da kuma Kenya, kuma ya yi kaurin suna wajen samun guguwar iska da ke dauke da ruwa.

A daidai wannan lokaci ana samun iska mai karfi da tsawa da kuma igiyoyin ruwa.

Masunta 5,000 suke rasa rayukansu a ko wacce shekara a cewar kungiyar agaji ta Red Cross.

"Da tsakar dare ake fara ruwan sama tare da iska mai karfi har zuwa karfe shida na safe," in ji Amone Ponsiano, jami'i a hukumar 'yan sandan teku a tsibirin Nkose da ke Uganda.

"A daidai wannan lokacin ne masunta suke shirye-shiryen shiga cikin ruwa. Aikin ne mai hadari sosai kuma akwai mutane da dama da suka bata."


Jami'in dan sanda Amone Ponsiano ya ce masunta da dama sun bata a lokacin da ake ruwan sama kamar da bakin kwarya
A baya-baya nan ne jirgin ruwan wani masunci ya yi karo da duwatsu lokacin da ya yi kokarin kauce wa mahaukaciyar guguwa, sai dai ma'aikatan Mr Ponsiano sun kubatar da shi daga cikin ruwa.

Sai dai wata sabuwar na'ura da masana kimiyya da fasaha daga kasashen ketare suka kirkiro watakila ta yi tasiri wajen kare rayukan daruruwan mutane.

Ana amfani da tauraron dan adam na hukumar kula da sararin samaniya ta Amurka wato NASA, wajen tattaro bayanan da ake amfani da su kan wata na'urar wadda ake amfani da ita wajen yin hasashen yanayi a kan ko za a iya fuskantar mahaukaciyar guguwa tare da ruwa.

Kuma za a yi amfani da na'urar ta hanyar aikewa da sako ga masunta ta shafin Twitter ko WhatsApp.

Farfesa Wim Thiery, jagoran bincike da aka yi tare da hadin gwiwar jami'ar Vrije ta Brussels, da jami'ar ETH Zurich ta Swizerland da hukumar NASA da kuma cibiyar CodeForAfrica sun ce akwai yiwuwar cewa sabbin fasahohi za su iya samar da na'urar inganta yadda ake hasashen yanayi.Guguwar iska mai dauke da ruwa a tafkin Victoria kan tayar da hanakli da janyo asarar rayuka
"Kamar sauran hasashen da aka saba yi, za a samu lokutan da za a samu sabani," in ji shi.

"Sai dai muna ganin nan gaba za mu inganta yadda mu ke hasashe kan matsanancin yanayi sakamakon kayan aiki na zamani da komfutoci da dubarun aiki da ake da su yanzu."

Amma kuma ba a Afirka kadai ba ne ake samun matsanancin yanayi.

A shekarar 2014, Ahmad Wani, dalibi ne da ke karatun injiniya a jami'ar Stanford wanda ya shafe mako guda yana jiran a kawo masa agaji, lokacin da aka yi ambaliyar ruwa a yankin Kashimir na Indiya.

Daruruwan mutane suka rasa rayukansu a ambaliyar ruwan.

Tun bayan aukuwar lamarin ya mayar da hankali wajen ganin ya yi amfani da basirarsa ta injiniya wajen kirkiro wata na'ura da za ta yi hasashe a kan illar da wata musiba ta ruwan sama ko girgizar kasa za ta janyo.

Ya yi amannar cewa mutane za su kasance cikin shirin ko ta kwana idan suna da cikakken bayani kan hasashen yanayi.

Ana samun asarar rayuka da lalacewar ababen more rayuka a duk lokacin da aka samu ambaliyar ruwa arewacin Indiya.
Mr Wani ya hada karfi da karfe da wasu abokan karatunsa su biyu inda suka kafa wani kamfani da ake kira OneConcern, domin nazari a kan yadda za a shawo kan matsalar.

"Kafin 2030, kashi 60 cikin dari na alumomin duniya zas u rika zama birane ," in ji shi, " inda mutane biliyan 1.4 zasu fuskanci hadarin aukuwar wani bala'i na ruwan sama ko gigiza kasa da sauransu.

Aman wuta ya kashe mutane a Guatemala
Wutar Daji ta kona gidaje a Ostreliya
A yanzu kamfanin na aiki tare da hukumomin Los Angeles da San Francisco a kan yadda za su inganta biranensu daga faruwar bala'i, kuma fatansu shi ne su kadammar da tsarin a sauran kasashen duniya.

"Burinmu shi ne mu ceto rayuka kuma mun yi amannar cewa na'urar zamani za ta taimaka mana," in ji Mr Wani.

Mutum takwas ne suka hallaka a wannan hanya da ke Tajikistan lokacin da zaftarewar dusar kankara ta afkawa wurin a 2017
Mutum 150 ne suke hallaka a ko wacce shekara sakamakon zaftarewar dusar kankara.

Sai dai yayin da kashi daya bisa biyu na yawan al'ummar duniya na amfani da waya kuma rabi daga cikin wayoyin komai da ruwanka ne, kuma Cibiyar AvyLab da ke nazari kan zaftarewar dusar kankara na ganin manhajar waya za ta taimaka hana aukuwar zaftarewar dusar kankara, da kuma aikin ceto mutane a lokacin hunturu.

"Manhajar waya kan zaftarewar dusar kankara ba wai za ta dakile yawan lamuran aukuwar zaftarewar dusar kankara ba ne," in ji Michael Murphy, wanda ya kirkiro AvyLab.

Ya kara da cewa: "Sai dai za ta ankara da al'ummar duniya ta hanyar samun bayanai da kuma tuntubar juna."

Fasaha
Ana amfani da fasaha wajen ankarar da mutane musibar da ke gab da aukuwa a kasashen duniya, domin kare rayukan mutane da rage barna da kuma yawan kudin da za a kashe kan kayan agaji.

Misali a kasar Mexico, kamfanin Start-Up Grillo ya kafa wata na'ura a cikin teku, wadda za ta ankarar da mutane a kan aukuwar girgizar kasa a manhajar wayar komai da ruwanka.

Ko da yake, mazauna yankin na da dakika 90 ne kawai na tattara ya-nasu-ya-nasu amma wadanda suka kirkiro na'urar sun ce wannan zai sa a kare rayukan mutane.
Daga Gabriella Mulligan
Wakiliyar BBC kan harkokin kasuwancin fasaha

No comments