Breaking News

Hotunan munanan gobarar daji da suka faru a duniyaGobarar daji ta yi barna sosai a wasu garuruwan da ke kusa da gabar teku a gabashin babban birnin kasar Girka, Athens.

Gomman mutane da suka hada da iyalai da yara sun mutu a yayin da suke kokarin tserewa gobarar.

Haka kuma wata gobarar dajin ta faru a Sweden, inda har ta kai nisan kusa Da'irar Arctic, kuma ta yi barna mai yawa a kasashen da suka hada da Portugal da Birtaniya da Amurka a watannin baya-bayan nan.

To ko me yake faruwa da ake samun irin wadannan gobara, kuma yaya za a magance faruwarsu?

'Busassun ciyayi na zama makamashin wuta'

Gobara na iya tashi hakan nan a daji, sakamakon zafin rana a yayin da ya bugi busassun ciyayi ko kuma idan tsawa ta fada dajin.

Sai dai kuma a cewar kwararru yawancin gobarar dajin da ake samu a duniya - kamar kashi 90 cikin 100 - mutane ne ke haddasa su.

Gobara na iya tashi idan aka zubar da garwashi ko guntun sigari ko ma toka mai zafi. Idan dai har akwai makamashin wuta a kusa, to nan da nan sai wuta ta tashi.


Iska mai karfi ta jawo tashin wuta a California


A wannan shekarar an yi hunturu mai busar da waje da ba a saba gani ba a kasar Girka, abun da ya jawo ciyayi suka bushe suka zama tamkar makamashin wuta, in ji Thomas Smith, wanda ya kusa zama farfesa a bangaren ilimin sanin kasa da muhalli a Kwalejin Tattalin arziki da Kimiyyar Siyasa ta Landan LSE.

Haka kuma rashin isasshen ruwan sama da iska mai karfi na sa wutar ta ta'azzara, ya dai danganta da karfinta da kuma inda take dosa.

Smith ya ce "Karmamin da ke ci da wuta na iya tafiya mai nisa ya watsu wasu sassan har wuta ta sake tashi."


23 ga watan Yuli: Busassun ciyayi na zama tamkar makamashin wuta yayin da aka yi gobarar ta Girka
Wutar da ta kama a kan dandaryar kasai kuwa ga misali, ba ta cika ruruwa da sauri ba, kuma an fi saurin tsayar da ita.

Wata kwararriya kan sha'anin wuta da ke zaune a Netherlands, Cathelijne Stoof, ta ce: "A takaice dai an ma fi son gobarar da ke tashi a dandaryar kasa, tana taimakawa tsirrai su sake fitowa."

"Matsalar ita ce, idan wutar ta fara kamawa daga kasan bishiya har zuwa sama, to ba fa za a iya dakatar da ita ba," in ji ta.15 ga watan Yuli: Gobarar daji 80 ce ta faru a Sweden saboda zafin rana
Thomas Smith ya yi bayani cewa mafi hatsarin ciki ita ce babbar gobara.

Ita ce wacce iska ke kara rura ta kuma kashe ta yana da wahaka saboda tsiri take yi sosai.


17 ga watan Yuli: Wannan hoton da aka dauka ta sama wanda Hukumar Sararain Samaniya ta Turai ta fitar na nuna yadda hakayi ke fitowa daga wasu gobarar daji da ta faru tsakanin yamma da gabar tekun Norway zuwa tsakiyar Swede. Babbar gobara na samar da bakin hayaki
Amma ba itace da ciyawa ne kawai ke kara rura gobarar daji ba. Gidaje da ababen hawan da ke kusa ma na rura wutar saboda suna dauke da makamashi irin na robobi.

                   Mai hadari


A Girka, motoci sun fi saurin kama wuta fiye da bishiyoyi, saboda motocin sun fi makamashi.24 ga watan Yuli: Hotunan motocin da suka kone sakamakon gobarar daji a kauyen Mati da ke kusa da Athens
Abun takaicin shi ne yadda mutane ke yawan mutuwa sakamakon gobarar a kokarinsu na tserewa.

Mafi yawan wadanda abun ya shafa a Girka sun makale ne a cunkoson motoci, yayin da mutane ke neman guduwa ko ta halin ka-ka, a cewar wani kwararre kan harkokin dazuzzuka, Alexander Held.

Amma za a iya gujewa hakan idan da an shirya yadda za a kwashe mutane a tsanake, in ji shi.23 ga watan Yuli: Hoton wani gida da ya kone kurmus saboda yana dauke da abubuwa masu makamashin wuta sosai a cikinsa
Zafi da hayaki na daga cikin munanan abubuwan da suka fi damun mutane a yayin da gobarar daji ta kama.

Haka kuma hayaki na yi wa masu ama da cututtuka irin na huhu da asma illa sosai.23 ga watan Yuli: An rufe hanya saboda yadda hayaki ya mamaye sararin samaniyar birnin Athens
Duk da cewa hayakin wutar mai guba ne, nan da nan yake bacewa.

Hayakin robobi da ledoji da ke samuwa a cikin gida ya fi hadari.A gobarar da ta faru kusa da Saddleworth Moor kuwa a Arewa Maso Yammacin Ingila, ba wajen da tsirrai ke fita ba ne kawai ya kama da wutar.


Gobarar Saddleworth Moor ta kai nisan kilomita 18 kuma ta shafe mako uku tana ci
Kashe gobara

'Yan kwanakwana na da jerin dabarun da za su iya amfani da su a kokarin kashe wuta ta hanyar hana ta shakar iska ko makamashi.

Suna bukatar horon da ya dace don sanin wacce za ta fi aiki.

A gobarar da aka yi a Birtaniya na baya-bayan nan, su kan yi amfani da abun duka ko tiyon ruwa don kashe wutar.


7 ga watan Disamba 2017: Wani jirgi yana jeho da abun kashe gobara a kusa da wani gida kusa da Los Alamos da Murrieta, da ke California, a watan Disambar da ya gabata
Kwararru sun ce daya daga cikin hanyoyin yakar gobara daji da suka fi tasiri ita ce yi wa wutar iyaka ta hanayar sare tsirrai ko bishiyoyi.21 ga watan Yuli: 'Yan kwana-kwana suna aiki don kashe gobara a dajin Stanislaus National Forest, kusa da gandun daji na Yosemite da ke California
Cathelijne Stoof ta ce: "Tawagogin da suka fi samun horo za su fi iya fahimtar yadda za su tunkari wuta kuma sun san hanya mafi dacewa ta yin hakan."
Gobarar Saddleworth Moor ta kai nisan kilomita 18 kuma ta shafe mako uku tana ci

Kashe gobara

28 ga watan Yuni: Masu kashe gobara na kokarin kashe wuta a kusa da Bolton, a Birtaniya
'Yan kwanakwana na da jerin dabarun da za su iya amfani da su a kokarin kashe wuta ta hanyar hana ta shakar iska ko makamashi.

Suna bukatar horon da ya dace don sanin wacce za ta fi aiki.

A gobarar da aka yi a Birtaniya na baya-bayan nan, su kan yi amfani da abun duka ko tiyon ruwa don kashe wutar.


7 ga watan Disamba 2017: Wani jirgi yana jeho da abun kashe gobara a kusa da wani gida kusa da Los Alamos da Murrieta, da ke California, a watan Disambar da ya gabata
Kwararru sun ce daya daga cikin hanyoyin yakar gobara daji da suka fi tasiri ita ce yi wa wutar iyaka ta hanayar sare tsirrai ko bishiyoyi.


Cathelijne Stoof ta ce: "Tawagogin da suka fi samun horo za su fi iya fahimtar yadda za su tunkari wuta kuma sun san hanya mafi dacewa ta yin hakan."
An Samo Data BBC Hausa

No comments