Breaking News

Ko Samar da wuraren kiwo zai hana rikicin makiyaya da manoma?Shanu na da matukar muhimmanci a wjaen Fulani ta yadda su kan yi tafiyar daruruwan kilomita don samar musu abinci
A cikin jerin wasikunmu na 'yan jaridar Afirka, babban editan jaridar Daily Trsut ta Najeriya, Mannir Dan Ali, ya duba yiwuwar ko samar da wuraren kiwo zai magance babban tashin hankalin da ake samu tsakanin manoma da makiyaya.

A yanzu haka dai babu wani batu da ke da zafi a Najeriya irin batun rikice-rikicen da ake samu tsakanin manoma da makiyaya - wadanda yawanci ke faruwa kan batun iko da filaye da damar yin kiwo.

A makon da ya gabata kadai an kashe mutum 200 a jihar Filato da ke arewa ta tsakiyar Najeriya bayan da aka shafe kwana uku ana rikici, wanda yawan wadanda suka mutu ya karu kan daruruwan da suka mutu a wannan shekarar kadai.Dama dai tuni jami'an tsaro na fama da rikicin Boko Haram a arewa maso gabashin kasar, suna kuma fafutukar samar da tsaro da kare yiwuwar kai hare-haren ramuwa.

Mutum 2,000 sun mutu a rikicin manoma da makiyaya
Ba a yi min adalci kan rikicin Fulani - Buhari
Ma'adanai na hada kan Fulani makiyaya da manoma a jihar Filato
Abun da na sani kan wannan rikici da aka shafe gwamman shekaru ana yi, ya kai shekara 50, a lokacin da wasu makiyaya masu dauke da adduna suka kai wa kauyena da ke jihar Katsina hari, a arewa maso yammacin Najeriya, inda suka ji wa mutane da dama rauni.

Amma wadannan hare-haren na yanzu sun fi muni fiye da na baya, saboda a yanzu makiyayan na da bindigogi.

Lamarin yana jawo gaba tsakanin al'ummu da kabilu a sassan kasar daban-daban, kuma ana kara matsawa gwamnati lamba ta yi wani abu.

A yanzu hukumomina shirin samar da wuraren kiwo.

Ana sa rana shirin zai sa makiyaya su dinga tsayawa waje guda don kiwon dabbobinsu su kuma daina kutsawa gonakin mutane don neman abinci ko ruwa, a yayin da yanayi ke sauyawa.

Wucewar dabbobi ta majalisar dokoki
Yawan al'ummar Najeriya na karuwa - kuma ita ce kasa mafi yawan jama'a a Afirka - wanda haka ke nufin mutane sun fara wuraren da aka ware domin kiwo.

Babban misali shi ne Abuja, wanda a cikin shekara 40 din da suka gabata ya zama gawurataccen babban birnin kasar daga dan karamin kauye da yake a baya.

Amma ta birnin ya ratsa ta daya daga cikin manyan burtalin kiwo kuma har yanzu makiyaya na bi ta wajen - a lokuta da dama shanu da motoci kan dinga gogayya kan wa yake da ikon bin hanya a manyan hanyoyin birnin.

A baya-bayan nan ma an dauki hoton wasu makiyaya suna ratsawa ta harabar majalisar dokokin kasar da shanunsu.


Kusan shekara guda bayan da aka yi batun samar da da wuraren kiwo, mataimakin shugaban kasa ya gana da gwamnonin jihohi sun kuma amince su tsara 94 daga wuarren kiwon a goma daga cikin jihohin kasar 36.

Wadannan za su kasance manyan filayen kiwo da za a sadaukar saboda kiwon shanu da tumaki.

Hakan kuma na nufin sai an gina makarantu da sauran abubuwan more rayuwa ga sabbin al'ummun.

Masu tsare-tsare sun kiyasta cewa zai dauki shekara 10 kafin a kammala smar da wuraren kiwon, a kan kudi naira biliyan 197.

Mannir Dan Ali

"Fulani mutane ne masu alfahari kuma dabbobinsu na da matukar muhimmanci a wajensu"


Sai dai kuma shirin na fuskantar kalubale masu yawa, da suka hada da zarge-zarge daga sauran kabilu, wanda yawanci 'yan bokon kasar ke rura wutarsa.

Wasu 'yan siyasa na mayar da batun rikicin kamar rikicin kabilanci, suna zarfin Shugaba Muhammadu Buhari, wanda Musulmi ne Bafilatani, da cewa yana neman hanyar da zai bai wa 'yan uwansa damar yin barna.

Ana kara rurar wutar wannan batu da cewa yawanci makiyayan Musulmai ne kuma Fulani da kuma cewa ai mafi yawan manoman Kiristoci ne daga yankin tsakiyar Najeriya.


Wasu jihohin kuwa tuni suka yi watsi da hakan don ba sa son samar da filayen.

Kungiyar Yarbawa zalla ta Afenifere ta ki yarda da shirin, tana mai cewa wurarem kiwon ba za su samu karbuwa a wajen al'ummar Yarbawa ba a kudu maso yammacin Najeriya, saboda suna zargin makiyayan za su mallake musu filayensu.

Sai dai duk da wadannan soke-soke da ake samu, ba gabatar da wata mafitar ba bayan wannan.Ana kuma zargin kafofin watsa labaran Najeriya da bayar da labaran rikicin inda suke nuna cewa makiyayan "makasa", suna kuma nuna cewa a kulluma su ne suke zalinci kuma ko da an zalinci makiyayan to ba za su ba da labarin hakan ba.

Hakan nan rahotannin da kafofin yada labaran kasar ke bayar wa suna kaucewa gaskiyar ainihin yadda rikicin yake.

Fulani mutane ne masu alfahari kuma dabbobinsu na da matukar muhimmanci a wajensu - su da iyalansu kan yi tafiyar daturuwan kilomitoci daga can arewacin Najeriya zuwa daya bangaren sau biyu a shekara, don su samu wajen da ya fi dacewa dabbobinsu su yi kiwo.

Shirin samar da wuraren kiwon bai yi la'akari da cewa zai sa nama ya yi wa 'yan Najeriya tsada ba don kuwa hanyar ciyar da dabbobin za ta kara tsada.

A yanzu haka ba a kashe wani kudin a zo a gani wajen ciyar da dabbobin tun da ciyawar da ke tsira aksa suke ci.

Shanu ba su mutane yawa ba
Su ma kuma Fulanin suna zargin da wata a kasa kan samar musu da wuraren kiwon don ba a wata hobbasa wajen ilimantar da su kan hakan da kuma yadda hakan zai amfane su nan gaba.

A yanzu haka su kan samar wa da 'yan Najeriya nama da madara da cukwi da dai sauran abubuwa da ake samu daga jikin shanu.Makiyaya suna dari-dari da shirin samar da wuraren kiwo
Wuraren kiwo ba sabon abu ba ne a Najeriya. An taba samar da wasu a lokacin Turawan mulkin mallaka kuma an ci gaba da amfani da su har zuwa shekarun 1980, a lokacin da aka rufe yawancin wuraren kiwon da gwamnati ta samra da ma na masu zaman kansu.

Babu dai wani bayani kan ko gwamnati ta duba dalilan da ya sa aka gaza a wancan lokaci - amma dai ga alama rashin kula ne ya jawo hakan.

Wani binciken da bai cika ba ya nuna cewa bambancin akwai tazara sosai idan aka kwatanta yawan jama'a da na shanu a Najeriya, ba kamar kasashe irin su Uruguay da Ajantina da Brazil, inda ake da wuraren kiwo masu yawa kuma yawan shanu ya fi na mutane.

Akwai kusan shanu miliyan 20 a Najeriya yayin da yawan mutane kuwa aka kiyasata da cewa ya kai mutum miliyan 200.

Amma ana bukatar a kara yin bincike don gamsar da masu adawa da samar da wuraren kiwon.

Kasar na bukatar yin bayani kan yadda hakan zai bunkasa tattakin arziki - da zai taimaka wa gwamnatin da ke son samar da wasu hanyoyin samun kudaden shiga daban da na man fetur.

Su ma kuma makiyayan akwai bukatar wayar musu da kai kan zargin da suke yi wa hukumomi kan batun da su kansu manoman da ke tsoron rasa gonakinsu.

Akwai kakkarfar bukatar karfafa bin doka da oda da gyara bangaren shari'a na miyagun laifuka, don a samu damar daukar mataki nan da nan kan barayin shanu da kuma hare-haren da ake kai wa al'ummomi.

Wannan ce kadai hanyar da za a magance irin wadannan hare-haren da ake kai wa nan da can, wadanda su ka sa rikicin ya yi muni.

No comments