Breaking News

Na fi Buhari cancanta saboda na fi shi ilimi – Tanimu Turaki

Daya daga masu neman jam'iyyar PDP ta tsayar da su takarar shugabancin Najeriya a zaben 2019, Kabiru Tanimu Turaki ya ce ya fi Buhari cancanta saboda "ya fi shi ilimi".

Kabiru Turaki wanda babban lauya ne da ke da matasayin SAN, yana daga cikin mutanen da suke fatan karawa da Shugaba Buhari idan APC ta tsayar da shi takarar shugabancin kasa.

Tsohon minista ne a gwamnatin PDP ta Goodluck Jonathan, kuma yana cikin 'yan jam'iyyar ta PDP da suka kasance a cikinta lokacin da take fama da rikicin shugabanci.

Turaki wanda ya fito daga jihar Kebbi ya ce ba za su samu matsala da sauran masu neman PDP ta tsayar da su takara ba, domin kuwa akwai fahimtar juna tsakaninsu.

Ya ce idan ya samu damar zama shugaban kasa zai yi abubuwa da dama da za su inganta rayuwar 'yan Najeriya.

Akwai dai wasu gaggan jam'iyyar ta PDP da dama da ke neman takarar shugabancin kasar a zaben na badi.

Tuni mutane kamarsu Sule Lamido, da Malam Ibrahim Shekarau, da Dr. Datti Babba Ahmad, da Alhaji Atiku Abubakar suka nuna aniyar yi wa jam'iyyar ta PDP takara domin karawa da Buhari na jam'iyyar APC.

Jam'iyyar PDP ta shafe shekara 16 tana mulkin Najeriya, kafin jam'iyyar APC ta karbe mulkin kasar a zaben shekarar 2015.

A bayan bayannan wasu 'yan majalisun kasar sun sauya sheka daga APC zuwa PDP, abin da ya sa wasu ke ganin hakan wani babban koma-baya ne ga jam'iyyar ta APC, musamman da yake watannin ne suka rage a gudanar da zabukan 2019.

Masu neman takara a PDP kawo yanzu

1. Atiku Abubakar
2. Ayo Fayose
3. Ahmed Makarfi
4. Sule Lamido
5. Malam Ibrahim Shekarau
6. Sanata Datti Baba-Ahmad
7. Gwamna Ibrahim Dankwambo

No comments