Breaking News

An Kammala Gidan Wutan Wudil Wadda Rht. HON. ENGR. MUHAMMAD ALI ya SamarAllahamdulillah Kamar yanda Hon Engr Muhammad Ali Wudil fnse Zabebben Danmajalisar Tarayya mai wakiltar kananan Hukumomin Wudil da Garko azauranmajalisar kasarnan tamu, Allah ya bashi ikon Kawowa al'umar yankunansa kabakin arzuki na gida Wuta Wanda Kananan Hukumomi guda bakwai 7 zasu amfana, bisa adda'oi da Al'umar wadannan Garuruwan keyi yasa Allah yasa aka kammala wannan aiki na GIDAN WUTA, Wanda zamuyi amfani da wannan damar mu sanar da al'uma halin da ake ciki dan gane da wannan Aiki na GIDAN WUTA, bisa Sahalewar mai girma Danmajalisar Tarayya Wudil da Garko Hon Engr Muhammad Ali Wudil fnse

Da farko Allah ya baiwa TRANSMISSION sun gama wannan aikin Wuta ta shiga Transformer.

Sai abu nana gaba, shine Fitar da'ita wannan Wuta daga transformer zuwa ga Transformer's Wannan aikin Distribution Company ne wato (KEDCO) wanda daka nan Zuwa Ko wanne lokaci zasu fara nasu aikin kuma suga sun kammala Cikin kankanin lokaci

Wanda tuni Mai girma Hon Engr Muhammad Ali Wudil fnse Ya lashi takwabin bibiyar su Dan su bada koda FEEDER 1 Ce dan jama'ar Wudil da Garko su fara amfana, Domin hakan zai bayar da dama aga yanayin Transformer din.


A karshe muke kara godewa al'umar wannan Gari bisa yanda suke ta adda"a tunda ka farkon fara wannan aiki har Allah yasa aka kammala Muna yiwa Allah godiya, muna yiwa mai girma Jajurtacce Danmajalisar Tarayya mai wakiltar kananan Hukumomin Wudil da Garko Engr Muhammad Ali Wudil fatan Alkairi da adda'ar Allah ya bashi sa'ar cin Zabensu a karo na hudu Ameen Thumma Ameen

     Sign Umar Da'u Danyaro

No comments