Breaking News

Atiku ya yi wa Buhari shagube: Zaben 2019


Atiku Abubakar a wurin zabe

Dan takarar shugaban kasar Najeriya a jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya bayyana cewa ya gamsu da yadda zaben Najeriya na 2019 ke gudana a ranar Asabar 23 ga watan Fabrairu.

Atikun wanda ya halarci mazabar tasa don kada kuri'a ya amsa tambayoyi daga 'yan jarida a kan yadda zaben ke gudana.

Dan takarar ya yi fatan Allah ya sanya a yi zabe lafiya a gama lafiya.

Zaben Najeriya: Za a yi ta ta kare tsakanin Atiku da Buhari

"Buhari mai mulkin kama-karya ne" — Atiku
Da aka tambaye shi ko zai amince idan ya fadi zabe, sai yace "kasan ni dan dimokradiyya ne ba kamar wasu ba."

Mutane da dama dai na ganin Atikun ya yi wa Shugaba Buhari shagube ne, wanda ya shaida wa 'yan jarida cewa ya san shi zai lashe zaben da ke gudana din.

Buharin dai ya riga Atiku kada kuri'a da safiyar Asabar din.

A ranar 23 ga watan Fabrairu ne 'yan Najeriya ke gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun kasar bayan dage zaben daga 16 ga watan Fabrairu.

Atiku da iyalinsa

'Yan Najeriya sun fita tun da safe domin kada kuri'unsu domin zabar wadanda suke so su jagoranci kasar tasu na tsawon shekara hudu mai zuwa.

No comments