Breaking News

Buhari ya ce ba zai fadi zabe ba Insha Allah

Buhari ya ce ba zai fadi zabe ba Insha Allahu


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce babu makawa shi ne zai lashe zaben shugaban kasar.

Da yake amsa tambayar wakilin BBC kan ko zai amince idan ya sha kaye, sai ya ce "ni zan ci zabe."

Buhari mai mulkin kama-karya ne — Atiku
Buhari da Atiku sun sake sa hannu a yarjejeniyar zaman lafiya
Shugaba Buhari ya kada kuri'arsa ce a birnin Daura da ke jihar Katsina tare ds mai dakinsa Aisha Buhari da rakiyar wasu jami'an gwamnatinsa.

Sai dai abokin hamayyarsa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce a matsayinsa na mai kare mulkin dimokradiyya zai yi biyayya ga sakamakon zaben kasar.

Wasu hotuna sun nuna yadda Shugaba Buhari ya kada kuri'a inda ya zabi kansa.Mai daukar hoto na kamfanin dillancin labaran Reuters ya dauki hotunan takardun kada kuri'ar Buhari, wadanda suka nuna cewa ya zabi kansa.No comments