Breaking News

Dage zabe: 'Najeriya ta yi asarar Dalar Amurka biliyan daya cikin kwana daya'
Dalilin da ya sa aka daga zaben shugaban kasa a Najeriya
Masana harkokin tattalin arziki sun ce dage zabukan da hukumar zaben Najeriya, INEC, ta yi ranar Juma'a da tsakar dare ya sa kasar ta yi asarar sama da $1bn cikin kwana daya kacal.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce sun dage zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisar dokokin tarayya daga ranar 16 ga watan Fabraitru zuwa ranar 23 ga watan Fabrairu.

Ya kara da cewa an dage zaben gwamnoni daga ranar biyu ga watan Maris zuwa ranar tara ga watan na Maris.Gabanin dage zaben, harkokin Najeriya sun tsaya cak inda aka rufe kan iyakokinta da kasuwanni da filayen jirgin sama da na kasa da dai sauransu.

Asara za ta shafi gwamnati mai zuwa

Sai dai a tattaunawarsa da BBC, wani masanin tattalin arziki Malam Aminu Dangana, ya ce dage zaben zai yi mummunan tasiri kan tattalin arzikin Najeriya.

"Shi tattalin arzikin Najeriya idan muka duba yadda aka kiyasta shi a 2018, wato a shekara guda 'yan kasar sun kirkiro arziki na $375bn, saboda haka idan ka duba rana guda idan aka bata ta, a takaice Najeriya ta yi asarar $1bn," in ji shi.

Ya kara da cewa wannan asara za ta shafi dukkan gwamnatin da ta lashe zaben da za a gudanar.

Da ma dai 'yan kasar sun soki hukumar zaben bisa dage shi, suna masu cewa bai kamata ta bayar da wani uzurin dage shi ba tun da shekara hudu ta yi tana shiri.

Sai dai hukumar ta ce ba da gangan ta dauki matakin ba, tana mai cewa da muguwar rawa gwara kin tashi.


Masanin tattalin arziki ya ce wannan asara da dage abe ya jawo za ta shafi dukkan gwamnatin da ta lashe zaben da za a gudanar.
Labarai masu alaka

No comments