Breaking News

KARATUN HAUSA A MATAKAN ILMI MAI ZURFI- PROF BUNZA


"Duk fafutukar da Hausa ta yi na kare martabar ilimi a Nigeriya, Turawan mulkin mallaka da 'yan barandarsu sun k'i sakar mata mara ta zama darasin ilmi mai cin gashin kansa. Ga zatonsu, barin Hausa ta mik'e k'afafunta a karatun boko wata kafa ce ta korar ingilishi da al'adun Nasara. Da hasken rana ya bayyana, d'aliban ilmi na Jami'ar Ahmadu Bello, Zariya, da ke Tsangayar Fasaha k'ark'ashin darusan Ingilishi da Larabci da Tarihi da Walwala da Ilimin siyasa su suka fara neman a ba Hausa gashin kanta a darusan Ilmin jami'a. Ta haka ne Hausa ta samu shiga jerin darusa masu karb'ar digirin kansu.
A lokacin da masu bitar tarihin karatun Hausa suka yi bitar bunk'asar karatun Hausa, Jami'o'in da ake koyar da Hausa fitattu uku ne. Amma a yau, muna da gawurtaccen cigaban karatun Hausa bisa ga cewa muna da:
1-Jami'o'in Tarayya takwas da ake karatun Hausa.
2-Jami'o'i na Jiha guda goma sha daya.
3-Kwalejin Ilmi na Tarayya guda sha hudu.
4-Kwalejin Ilmi na Jiha guda sha bakwai.
5-Manyan makarantun Fasaha guda bakwai.
6-Cibiyoyin bincike na Tarayya guda hudu.
A wannan k'arni da muke ciki, babu harshe daga cikin harsunan Afirka da ke da makusanciyar rabin wad'annan makaman Ilmi. A gida Nigeriya, ko ba a gwada ba linzami ya fi k'arfin bakin kaza."- 
Prof Bunza

No comments