Breaking News

'Yan Najeriya miliyan 11 ba za su kada kuri'a ba- INEC


 Jerin masu kokarin kada kuri'a a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun Najeriya, a unguwar Ja'in da ke jihar Kano; tsugunne a gefe guda wani gurgu ne tsugunne a gefen layin masu zaben, saboda rashin samar da layi na musamman domin masu fama da nakasa.

A dai dai lokacin da al’ummar Najeriya ke kada kuri’a a babban zaben kasar da ke gudana a yau Asabar, hukumar zaben kasar mai zaman kanta INEC, ta ce fiye da mutane miliyan 11 ba za su samu damar kada kuri’a ba, saboda gaza karbar katunan zabensu na din-din-din.

Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Yakubu Muhmud, ya ce akalla ‘yan Najeriyar miliyan 11 da dubu 228 da dari 582 basu samu damar karbar katunan zabensu na din-din-din ba, har zuwa lokacin da hukumar ta rufe karba.

A cewar Farfesa Mahmood Yakubu kashi 86 da digo 63 cikin 100 na adadin masu rijistar zaben a Najeriya ne kadai suka karbi katunan zaben su, batun da ke nuna cewa akwai kashi 13 da digo 37 da suka gaza karbar katinan.

INEC ta ce adadin ‘yan Najeriya da suka yi rijistar zaben ya kai mutane miliyan 84 da dubu 4 da 84, yayinda miliyan 11 da dubu 228 da dari 582 suka gaza karba, matakin da ke nuna cewa mutane miliyan 72 da dubu 775 da dari 502 ne kadai suka cancanci kada kuri’a a zabukan na yau.

Hukumar ta bayyana cewa jihohin Lagos Kano da Ogun, su ne kan gaba wajen yawan mutanen da basu karbi katunan zabensu ba, inda ta ce a jihar Lagos kadai akwai adadin mutane miliyan 1 da dubu 38 da dari 902 da basu karbi katin ba, sai jihar Kano da dubu 761 kana jihar Ogun da adadin dubu 680 da 136.

No comments