Breaking News

2023 YADDA KWANKWASIYYA ZA TA KAR'BI RAGAMAR MULKIN KANO DA MA NAJERIYA BAKI DAYA. ...daga alkalamin Tijjani Muhammad Musa
Yanzu dai kowa ya kwana da sanin abubuwan da su ka gudana a za6en Gwamnoni na 2019 da hukumar gudanar da za6e ta kasa wato INEC ta gudanar inda a Jihar Kano wata sabuwar kalma wai ita inkonkulusib ta kunno kai ta kuma taka wata muhimmiyar rawa wajen fiddawa jihar wanda zai rik'i ragamar tafiyar da al'amuranta nan da shekaru hud'u ma su zuwa.

Na kuma ji jawabin bayan za6e da Sen. Rabiu Kwankwaso, madugu wannan aqida ta Kwankwasiyya ya yi ana karad'a shi a kafar sadarwa ta soshiyal midiya inda ya nuna bak'in ciki, 6acin rai da takaicin abinda ya faru a lokacin da aka gudanar a lokacin za6en nan na inkonkulusib wanda ya zo ya wuce ranar 23 ga watan Maris, 2019.

Toh ni dai ba dan Kwankwasiyya ba ne, siyasata kowa ya sani ta Buhari ce. Amma nazarin da na yi wa tafiyar siyasar Madugun Kwankwasiyya da irin rawar ganin da kokarinsa na kafawa Abba Gida-gida gwamnati da ya yi, da yadda haqqansa ta kusa cimma ruwa ya sa na yi wani tunani inda na ga dacewar in bayyana ra'ayina game da siyasar 'yan Kwankwasiyya.

Ta haska mu su hanyar da za su bi in har su na so Kwankwasiyya a matsayinta na aqida ta dore kai harma su samu damar kafa gwamnati, ba ma a Kano kawai ba, kusan a kowacce jiha a fadin tarayya. Akwai ni da ta cewa da yawa amma a wannan ga6ar ga abinda na ke ganin zai fishshe ma su burin ganin Kwankwaso ya kafa jagoranci mai d'orewa nan gaba.

Abubuwa ne guda goma (10) ma su sauqi amma kuma ma su wuya ya danganta da yadda aka dauki kudurin cimmusu. Amma da in bar su a tare da ni ina ganin gwara in bayyanasu ko Allaah zai sa su amfani Kwankwaso da ma sauran mabiyansa na aqidar Kwankwasiyya mazansu da matansu. Ga su kamar haka...

1. Ta tafi kotu kalubalantar sakamakon za6en raba gardamar Gwamna ta 2019. Kar su damu da cin nasarar kwatar mulkin daga hannu Ganduje, amma duniya ta shedi cewa ita ma tafiyar Kwankwasiyya ta ma su neman haqqinsu ne ta hanyar da ta dace wato ta fannin bin doka da oda, kuma ta hanyar shari'a. In ta yi ruwa rijiya, in ba ta yi masai.

2. Su koma gida su sake lale. Tun da tafiyarsu ta aqida an dorata ne akan gina matasa da mata, toh su maida wannan manufa ta zam ginshiqin madogararsu. Ala ayya halin, matasa da mata sun zam jigon tafiyar Kwankwasiyya a duk inda su ke tallarta.

3. Su yi wa tafiyar Kwankwasiyya rajista a matsayin jam'iyar siyasa mai zama da cin gashin kanta. Duk wani raka6e-raka6e su daina. Su bi jihohi, birane, garuruwa dabandaban na kasar nan su samu wakilci da ofis-ofis da adireshi. Ta hakan in Kwankwaso ya na son ya yi takarar shugabancin Najeriya ba sai ya tsaya ya na wani raragefe ba. Kuma sai wanda ya lamuncewa zai zama dantakara a jam'iyarsu ta Kwankwasiyya Party.

4. Su nemi wasu matasa daga cikin wadanda ya amfanar da mulkinsa ta hanyar daukan nauyin iliminsu, masu hankali, natsuwa, kaifin basira, hangen nesa, hazaqa, ilimin boko da na addini da dai sauransu, wanda su ka iya mu'amalat da jama'a ta kowacce fanni, kuma daga ko'ina su dora su akan kudurinsu na neman mulkin jihar Kano ko wata jiha kai ko ma kasarnan baki daya. Madugunsu ya koma bayan fagge, a daina jinsa barkatai, a daina ganinsa araha. Amma fa duk wani motsi ko furucin da za su yi, toh ya zam shi ne kat! Maganarsa ta zam sai akan wasu muhimman abubuwa.

5. Ya kamata kuma su koyi gudanar da damokaradiyyar cikin gida. A bari kowa ya nuna buqatarsa ta yin takara a siyasar cikin gida. Duk wani Bakwankwashe ko Bakwankwashiya su fito su gwada farin jininsu da kar6uwa a wajen sauran Kwankwasawa. Wannan k'ak'abawa mabiya d'antakara kamar yadda aka yi a baya, sam bai yi ba. Dalilin da ya sa wannan shawara ta fito shine in mutanen Kwankwasiyya za su lamunci biyayya ga Madugunsu, toh in aka shiga fagen siyasar du gari, ba lalle sauran 'yan siyasa su yarda da wani d'orin d'osano ba. Sannan 'yan Kwankwasiyyan ba za su goge ko su saba da gasar fidda gwani ba.

6. Su nemi hanyoyin yad'a aqida da manufa ta kafofi dabandaban daga irin na daa da na zamani. Sannan su samu kwararru akan fanni sadarwa su dora mu su nauyin k'irk'iro da kuma fadakar da al'uma shin mecece Kwankwasiyya, daga ina ta ke, a ina ta ke yanzu haka kuma ina ta dosa?

7. Daga nan su nemi 'yan Kwankwasiyya musamman matasa maza da mata su dinga shiga takara a kowane mataki da rukuni, na 'yan majalisun jihohi, gwamnoni a jihohi da wakilai da sanatoci a tarayya baki daya don cimma buri da manufar kawo sauyi a mulki da ci gaban al'umma, ba tare da nuna bangaranci, kabilanci, banbancin jinsi, addini ko aji ba. Su gina wannan za6i akan cancanta, kwarewa da kuma iya jagoranci.

8. Sannan kuma su na mulki ba sa mulki akwai bukatar a dinga jinsu ana ganin hannunsu a cikin assasa aniyarsu akan al'umar da su ke burin su mulka ta yi mu su hidima da kai mu su d'oki, tallafi, kula da dai sauransu ta hanyar kafa wata gidauniya mai zaman kanta. Wacca a koda yaushe za ta dinga aiwarar da ayyukan alkhairi ga matasa, mata da talakawan gari wanda su ne su ke za6e. Ta haka da an ce "Ina matasaaaa!?"

9. Sannan duk wani matsayi na shugabanci su shiga a dama da su don tabbatar an yi adalci da abinda ya kamata cikin lamarin. Sannan in Allah Ya ba su cin nasarar shiga majalisun nan, toh su tabbatar sun yi wa Kwankwasiyya kyakkyawar wakilci. Su zama jakadai da za a dinga koyi da su ana sha'awar kwaikwayonsu. Ba kamar yadda ake samun akasin haka ba a yanzu. Inda banda miyagun maganganu da tsinuwa da nuna rashin tawakali, babu abinda ake yi wa da yawa daga cikinsu shaida da shi a wannan marrar.

10. Su tabbatar duk wani lamari da aka ce akwai wani d'a ko 'yar Kwankwasiyya a cikinsa a majalisun nan na jiha ko ta kasa baki d'aya sun yi fice a ciki ta fanni ba da gudummawarsu don cimma nasarar abin da aka sa a gaba. Wannan zai sa su zama wasu abin kiyayewa, nuni da samun natsuwa a tattare da gaskiya, jajircewa, bin ka'ida, da kuma tasirinsu. Wato a duk kudirinsu su tuna Allaah, sannan su maida al'amuransu gare Shi ba kowa ba kuma ko komai ba.

Toh in har za su iya yin wadannan abubuwa, abu ne mai sauqi cikin dan lokaci kankani su samu nasarar cimma burinsu in sha Allaah. Amma duk wani abu ko wata hanya akasin wadannan, ba zan ce haqarsu ba za ta cimma ruwa ba, amma za su dade ba su samu yadda su ke so ba. Sai dai kuma Allaahu A'lam.

Bissalaam

1 comment: