A shirye muke tsaf mu hadu da Atiku a Kotu – APC - DWGUNSAU'S BLOG

Breaking

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Wednesday, 6 March 2019

A shirye muke tsaf mu hadu da Atiku a Kotu – APC


Jam'iyyar APC ta ce a shirye ta ke ta kalubalanci dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar a Kotu.

APC ta nesanta kanta da wasikar da wata kungiyar yakin neman zaben Buhari ta rubuta wacce ta nemi kasashen duniya su hana wa Atiku zuwa Kotu domin kalubalantar nasarar sake zaben shugaba Buhari

Sanarwar da Barista Festus Keyamo mai magana da yawun ofishin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar APC ya fitar ranar Talata ta ce babu yawun jam'iyyar APC ko shugaba Buhari a matakin da kungiyar ta dauka.

Keyamo ya ce duk abin da kungiyar ta fitar bai shafi ofishin yakin neman zaben shugaban kasa ba na jam'iyyar APC ko shugaba Buhari ba.

"Mun matsu ma mu hadu da Atiku a Kotu domin mu tabbatar wa duniya yadda ya sha kashe a sahihin zaben," in ji shi.

APC ta ce kungiyar tana da 'yancin fadin albarkacin bakinta amma ba shi ne matakin jam'iyyar ba a hukumance.

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad

Responsive Ads Here