Breaking News

Abdullahi Umar Ganduje ne ya lashe zaben gwamna a Kano

Abdullahi Umar Ganduje ne ya lashe zaben gwamna a Kano


Maigirma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje

An sake gudanar da zaben Kano ne a wasu mazabun kananan hukumomi 28
Abdullahi Umar Ganduje na jam'iyyar APC ya lashe zaben gwamna a jihar Kano a wa'adin shugabanci na biyu, kamar yadda hukumar zabe (INEC) ta bayyana ranar Lahadi.

Ganduje ya kayar da Abba Kabir Yusuf dan takarar babbar jam'iyyar hamayya ta PDP, bayan sanar da sakamakon zaben jihar da aka kammala a ranar Asabar 23 ga watan Maris.

Gwamna Ganduje ya lashe zaben ne da tazarar kuri'a 35,637 inda jam'iyyarsa ta APC ta samu kuri'a 45,876 yayin da PDP ta samu 10,239.

Yanzu jimilla, APC ta samu kuri'a 1,033,695, yayin da PDP ta samu jimilla 1,024,713. Hakan na nufin Ganduje ya lashe zaben ne da tazarar kuri'a 8,982.

Sai dai jam'iyyar PDP reshen Kano ta yi watsi da sakamakon zaben na gwamna da aka kammala.


Zaben Kano dai ya ja hankali bayan sanar da da ba a kammala zaben ba a ranar Asabar 9 ga watan Fabrairu.

A zaben 9 ga watan Maris da aka gudanar PDP ce kan gaba da tazarar kuri'a sama da dubu 26.

An sake gudanar da zaben Kano ne a wasu mazabun kananan hukumomi 28.

Jam'iyyar APC ta lashe zaben a rumfunan kananan hukumomi 27 da aka sake zaben, yayin da PDP ta lashe karamar hukumar Dala.

Waiwaye


A zaben 9 ga watan Maris da aka gudanar PDP ce kan gaba da tazarar kuri'a sama da dubu 26
Rabi'u Musa Kwankwaso shi ne ubangidan Abba Kabir Yusuf a siyasance, kuma akwai takun saka sosai tsakaninsa da Gwamna Ganduje wanda a baya ya yi masa mataimakin gwamna har sau biyu.

A lokacin da PDP ta tsayar da Abba a matsayin dan takararta Kwankwaso ya sha suka a ciki da wajen jihar, inda ake zarginsa da cewa ya tsayar da surukinsa a matsayin dan takara.

Maimakon tsohon mataimakin Ganduje, Hafiz Abubukar da suka bata ya kuma koma wajen Kwankwaso.

Sai dai Kwankwason ya ce Abba ba mijin 'yarsa ta cikinsa ba ne mijin 'yar wansa ce, kuma bai tsayar da shi don radin kansa ba sai don ganin mutum ne da zai yi wa jihar Kano aiki bisa kishin kasa da jajircewa, sannan kuma "ba zai yi masa butulci ba."

Yawan masu kada'a kuri'a a Kano
Kano dai ita ce ta biyu a yawan wadanda suka yi rijistar zabe a Najeriya bayan Legas, inda mutum miliyan 5,457,747 suka yi rijista amma mutum 4,696,747 daga ciki ne suka karbi katunansu na zabe.

Sannan kuma a jihar ba a samu raguwar masu kada kuri'a sosai ba idan aka kwatanta da na zaben shugaban kasa, ba kamar wasu jihohin ba da raguwar masu kada kuri'ar ya yi kasa sosai idan aka kwatanta da na zaben shugaban kasar.

No comments