Ajax ta yi waje "road" da Madrid a Champions League - DWGUNSAU'S BLOG

Breaking

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Wednesday, 6 March 2019

Ajax ta yi waje "road" da Madrid a Champions LeagueAjax ta yi waje road da real Madrid, bayan da ta ci 4-1 a wasa na biyu zagaye na biyu a gasar cin kofin Zakarun Turai da suka kara a Santiago Bernabeu ranar Talata.

Ajax ce ta fara cin kwallo ta hannun Hakim Ziyech minti bakwai da fara wasa, sannan David Neres ya kara na biyu minti 11 tsakani, kuma haka aka je hutu.

Bayan da 'yan wasa suka sha ruwa suka dawo fili ne Dusan Tadic ya kara na uku daga baya Marco Asensio ya ci wa Madrid kwallo.

Sai dai kuma minti biyu tsakanin kwallon da Asensio ya ci ne Ajax ta kara na hudu ta hannun Lasse Schone a bugun tazara.

Real ta karasa wasan da 'yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Nacho Fernandez jan kati daf da za a tashi daga fafatawar.


A wasan farko da suka buga a Netherland a cikin watan Fabrairu Real Madrid ce ta ci 2-1, jumulla Ajax ta ci kwallo 5-3.

Ajax ce kungiyar farko da ta ci kwallo hudu a Santiago Bernabeu tun bayan 2015 lokacin da Barcelona ta doke Real da ci 4-0 a wasan La Liga ranar 21 ga watan Nuwambar 2015.

Karon farko da Real Madrid ta kasa kai wasan daf da na kusa da na karshe tun bayan shekara tara a gasar ta Champions League.

Ita kuwa Ajax wannan ne karon farko da ta kai wannan matakin tun kakar 1996/97, kuma kungiyar ta Netherland tana da kofin Zakaraun Turai guda hudu a tarihi.

Real Madrid ta yi ban kwana da Copa del Rey da na Zakarun Turai tana ta uku a kan teburin La Liga da tazarar maki 12 tsakaninta da Barcelona ta daya.

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad

Responsive Ads Here