Breaking News

Amurka ta ki dakatar da amfani da jirage kirar 'Boeing 737 Max'

Amurka ta ki dakatar da amfani da jirage kirar 'Boeing 737 Max'Sanata Ted Cruz ya ce yakamata AMurka ta yi tunani domin dakatar da amfani da wannan jirgin har sai an yi bincike
Hukumar da ke kula da sufurin jiragen sama ta Amurka ta bayyana cewa kasar ba za ta dakatar da amfani da jirgi kirar ''Boeing 737 Max'' ba duk da irin wutar da aka huro mata daga bangaren sanatoci da kuma kungiyoyin ma'aikatan kasar.

Hukumar ta bayyana cewa an yi bita a kan yanayin aikin jirgin kuma ba a gano wata matsala tattare da shi ba, saboda haka babu hujjar dakatar da amfani da jiragen.

Ted Cruz dan jam'iyyar Republican wanda shi ne shugaban kwamitin da ke kula da sufurin jiragen sama na majalisar dattawa a Amurka ya ce: ''Ina ganin ya kamata Amurka mu yi tunani domin dakatar da amfani da wannan jirgin har sai hukumar da ke kula da sufurin jiragen sama ta tabbatar da ko za a iya amfani da jirgin domin ci gaba da daukar fasinjoji ba tare da wata matsala ba.''

Tarihin Jiragen

Haka ma a daya bangaren 'yan jam'iyyar Democrats da suka hada da Edward Markey da Richard Blumenthal sun rubuta wa hukumar da ke kula da sufurin jiragen sama ta Amurka inda su ma suka yi irin wannan bukata ta Sanata Ted Cruz.

Amma a nata bangaren hukumar da ke kula da sufurin jiragen ta ce sauran hukumomi masu sa ido a kan lafiyar jiragen sama a kasar ba su yi wani sahihin bayani ba da zai zama hujjar dakatar da amfani da jirgin ba.

A ranar Lahadi ne wani jirgi na kasar Ethiopia ya yi hatsari inda mutane 157 suka rasa ransu da suka hada da fasinjioji 149 da ma'aikata takwas kamar yadda kamfanin ya bayyana.

Jirgin yana dauke da fasinjoji 149 da ma'aikata takwas, kamar yadda kamfanin jirgin ya bayyana.

Fasinjoji 32 da ke cikin jirgin 'yan kasar Kenya ne, sai 18 'yan Canada, da takwas 'yan Amurka, sai kuma bakwai 'yan Burtaniya.

Wannan hatsarin na zuwa ne watanni biyar bayan irin samfarin jirgin na kasar Indonisiya ya yi hatsari.

A yanzu haka kasashe da dama da suka hada da Burtaniya da Kasashen Tarayyar Turai da Australia suka dakatar da amfani da wannan jirgi tun bayan hatsari na biyu da ya yi a ranar Lahadi.

A ranar Laraba ne Hong Kong da da Vietnam da New Zealand suka shiga jerin kasashen da suka dakatar da amfani da samfarin jirgin 737 Max.


No comments