Breaking News

Duk wanda ya ci zaben Kano a ba shi kawai - Bashir Tofa

Duk wanda ya ci zaben Kano a ba shi kawai - Bashir Tofa


Fitaccen dan siyasa a Najeriya Bashir Othman Tofa ya yi kira ga 'yan takarar zaben gwamna a jihar Kano da su rungumi kaddara ga duk wanda ya fadi zabe.

A hirarsa da BBC, Alhaji Bashir Tofa wanda shi ne shugaban wata kungiyar ci gaban Kano, ya bayyana fargabar tashin hankali a Kano idan har aka nemi sauya sakamakon zaben da za a sake a wasu mazabu.

"Yanzu hakkin INEC ne ta fitar da abin da yake shi ne halal wanda za a yadda da shi ko da an tafi kotu," in ji shi.

Ya kuma yi kira ga 'yan takarar manyan jam'iyyun siyasar Kano da su ja hankalin magoya bayansu domin ganin an gudanar da zaben lafiya.

A ranar Asabar 23 ga watan Maris ne hukumar INEC ta ce za ta sake yin zabe a wasu mazabu a Kano bayan sanar da cewa ba a kammala zaben jihar ba da aka gudanar a ranar 9 ga Maris.

Fafatawar a zaben da za a sake a Kano ta shafi 'yan takarar manyan jam'iyyu biyu ne gwamna Ganduje na APC da kuma babban mai hamayya da shi Abba Kabir Yusuf na PDP.

Siyasar Kano na ci gaba jan hankali, saboda girman hamayya tsakanin manyan jam'iyyun siyasa guda biyu APC da PDP.

Alhaji Bashir Tofa ya taba takarar shugaban kasa a 1993 a jam'iyyar NRC zamanin zamanin mulkin soja na janar Ibrahim Badamasi Babangida.

Ya ce yana fatan sake zabukan da aka soke ba zai haddasa wani tashin hankali ba a Kano


No comments