Breaking News

Gwamna Lalong ya lashe zabe a Filato

Gwamna Simon Lalong ya lashe zabe a Filato

Gwamna Simon LalongHukumar zabe a Filato ta tabbatar da Gwamna Simon Lalong na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar bayan sanar da sakamakon zaben da aka kammala.

Lalong ya kada tsohon ministan Abuja Jeremiah Useni na jam'iyyar PDP.

An gudanar da zaben ne a mazabun kananan hukumomi tara wadanda ba a kammala ba a zaben farko na gwamna da aka gudanar a ranar 9 ga Maris.

Jam'iyyar APC ta lashe kananan hukumomi guda shida a mazabun da aka sake zaben. Jam'iyyar PDP kuma ta lashe kananan hukumomi uku.

Yanzu APC ta lashe kananan hukumomi 11 cikin 17 na jihar Filato yayin da PDP ta lashe kananan hukumomi guda shida.

Filato na cikin jihohin da suka ja hankali ake karasa zabukan gwamnoni wadanda suka hada da Bauchi da Benue da Kano da kuma Sokoto.

No comments