Breaking News

Gwamna Mohammed Abubakar: 'Dalilin da ya sa na fadi zabe'

Gwamna Mohammed Abubakar: 'Dalilin da ya sa na fadi zabe'Dan takarar jam'iyyar APC kuma Gwamnan jihar Bauchi Mohammed Abdullahi Abubakar ya bayyana wa BBC dalilin da ya sa ya fadi zaben gwamnan jihar.

A wata hirar da ya yi da BBC a Abuja ranar Talata, gwamnan ya ce Allah ne ya san dalilin da ya sa ya fadi zaben.

Sai dai ya ce ya ci zabe a yawancin kananan hukumomin jihar, "idan ban da guda biyu wadanda aka yi aringizon kuri'u," a cewarsa.

"Don haka sakamakon zaben ba ya nuni da cewa al'ummar jihar ba sa sonmu, don mun yi abin so. Idan aka shiga lungu da sako, za a ga wani aiki da gwamnatin APC ta yi," in ji shi.


Gwamnan ya ce tuni ya taya wanda ya lashe zaben murna, kuma ya bukaci ya ja hankalin magoya bayansa yayin da suke murnar cin zabe domin "kada a tayar da hankalin jama'a."

Har ila yau, ya ce ya yi farin ciki yadda aka gudanar da zabukan ba tare da an samu tashe-tashen hankulan jama'a ba.

"Allah ne ke ba da mulki ga wanda yake so, kuma shi ne mai karba daga hannun wanda yake so, a lokacin da yake so," in ji shi.

Ya ci gaba da cewa wannan ne dalilin da ya sa ya taya abokin hamayyarsa murnar samun nasara.

Hakazalika ya ce shi ba zai kalubalance sakamakon ba a gaban kotu, sai dai ya ce jam'iyyarsa tana da hakkin kalubalantarsa.

Sanata Bala Muhammad ya doke gwamnan ne da bambanci kuri'u 14,488.

A zaben da aka gudanar a jihar, PDP ta samu jimullar kuri'u 515,113, yayin da APC da ke mulki a jihar ta samu kuri'u 500,625.

An samu tsaiko dai kafin kammala zaben, inda har hukumar zabe INEC ta bayyana zaben jihar a matsayin wanda bai kammala ba.

No comments