Breaking News

Gwamnatin Pakistan na farautar 'yan kungiyar JEM

SHUGABAN JEM Masood Azhar

Hukumomi a Pakistan sun kama wasu 'yan uwan shugaban kungiyar Jaish e Mohammad - kungiyar da ta dauki alhakin kai harin kunar bakin wake kan sojojin Indiya a Kashmir.

Wannan harin ya janyo rikici tsakanin kasashen biyu a yankin Kashmir.

Amma gwamnatin ta Pakistan ta ce ta dauki matakin ne domin radin kanta, ba domin an matsa ma ta daga waje ba.

Pakistan ta sanar da cewa ta kama wani dan uwa da dan Masood Azhar, mutumin da ya kafa kungiyar nan ta Jaish e Mohammad domin abin da gwamnatin ta kira binciken da dalilam tsaro.

Sakataren harkokin cikin gida na kasar Azam Suleman Khan ne ya bayyana matakin kuma ya ce idan gwamnati ta gano wata shaida cewa suna da hannu a harin da aka kai kan dakarun Indiya, to gwamnati za ta hukunta su.

Harin ya janyo riic mafi muni tsakanin kasashen biyu wadanda makwabta ne kuma sun dade suna rigima akan wanda ke da iko a yankin na Kashmir.

An kuma tsare da wasu mambobin kungiyar 42, kuma ana jin wasunsu na cikin wata takardar tuhuma da Indiya ta mika wa Pakistan kan harin kunar bakin waken da aka ki a watan jiya.

Abin lura a nan shi ne Pakistan ta sha kama irin wadannan mutanen a baya, amma sai ta sake su ba tare da an yanke masu hukunci ba.

No comments