Breaking News

Jerin sunayen sanatocin da za a ba takardar shaida a Abuja

Jerin sunayen sanatocin da za a ba takardar shaida a Abuja

Akwai sanatoci 109 a majalisar dattawan NajeriyaHukumar zaben Najeriya INEC ta ce za ta ba sanatoci da 'yan majalisar wakilai takardar shaidar lashe zaben ranar 23 ga watan Fabrairun bana.

Sai dai hukumar ta ce wadanda sunayensu suka bayyana a shafinta na Intanet ne kawai za ta bai wa takardar.

Kawo yanzu sanatoci 100 ne cikin kujeru 109 da kasar take da su hukumar ta bayyana sunayensu.

Kodayake ta ce za ta sanya sunayen sanatocin wadanda suka lashe zabukan da aka sake yi a ranar 9 ga watan Maris.

A halin yanzu cikin sanatoci 100 da aka bayyana sunayensu - 62 'yan jam'iyyar APC ne, sai 37 na jam'iyyar adawa ta PDP da kuma guda daga jam'iyyar YPP.

Ga jerin suanayen sanatocin kamar haka:No comments