Breaking News

Ko kun san jaruman India masu saurin kuka?

Ko kun san jaruman India masu saurin kuka?

Yin kuka a fim ga jarumai ba ani abon abu bane, a kansa mutum ya yi kuka a fim kamar gaske.

To amma da wuya kaga wani jarumi ko jaruma sun yi kukan gaske a bayyanar jama'a.

To sai dai kuma a zahiri akwai jaruman da za a ga suna tausayi lamarin da ke sa su saurin kuka ko a gaban waye.

Ga wasu daga cikinsu:


Deepika Padukone

Deepika Padukone, na daga cikin jaruman fina-finan India da ta ke da saurin kuka.

Ba sau daya ba ba sau biyu ba, ta sha yin kuka a gaban mutane.

Deepika ta taba yin kuka a lokacin da ta ke karanta wata wasika da mahaifinta ya bar mata bayan ta karbi wata lambar yabo da aka bata.

Kazalika ta taba yin kuka a bayyanar jama'a bayan ta bayar da labarinta a kan irin damuwar da ta shiga a rayuwarta.


Alia Bhatt

Jaruma Alia Bhatt, tana da raunin zuciya domin abin kuka ba ya mta wuya.

Ko wani abu na farin ciki ta tuna wanda ya shafeta, ta kan yi hawaye, haka idan na bakin ciki nema.

Ga ta kuma da tausayi, idan taga abin tausayi wanda ya shafi mutane musamman marassa karfi, ta kan yi kwalla.Rani Mukherji

Ga wadanda ke kallon fina-finan India, sun an cewa a yanayin Rani dama mace ce mai ruwan salihai.

Duk da cewa ta na da saurin fushi, Rani abin tausayi ba ya mata kadan.

Itama ta yi kuka a gaban bayyanar jama'a ciki har da wajen bikin raba lambobin yabo.

Akwai wani biki makamancin wannan da aka yi a baya inda aka taba batun fitaccen mai shirya fim da bayar da umarni Yash Chopra, kan ka ce me Rani ta fara kuka shame-shame, saboda ta tuna irin gudunmuwar da ya bayar wajen daukakarta a harkar fina-finan kasarsu.

Ire-iren wadannan abubuwa idan ta tuna, ta kan yi hawaye ko a gaban waye.


Salman Khan

Salman Khan na daga cikin jarumai maza da suke da zuciya da mai rauni.

Abin kuka ba ya masa wuya domin ya taba kuka a wajen wata gasar rawa ta yara inda wani yaro ya rera daya daga cikin tsoffin wakokin fim dinsa.

Kazalika ya sha kuka a lokuta da dama musamman a lokuan da ake yanke masa hukunci sakamakon wasu laifuka da ya yi a baya.

Haka idan ya ga wani a cikin mawuyacin hali, na lalurar rashin lafiya ko kuma talauci, ya kan zubar da hawaye.

Wannan ne ya sa ya ke yawan taimakawa mutane da kudadensa.


Aamir Khan

Jarumi Aamir Khan ma kuka baya masa wuya, domin mutum ne mai tausayi.

Sau da dama idan yaje gidn kallo domin kallon wani sabon fim da za a haska, in dai a cikin fim din akwai abin tausayi, to lallai kam za a ga Aamir Khan na share hawaye.

A wasu lokutan ma ya kan bar gidan kallon idan ya ga ba zai iya karasa kallon fim din ba.

Aamir Khan, ya yi kuka a lokacin da aka haska fim din Bajrangi Bhaijaan na Salman Khan.


Sanjay Dutt

Sanjay Dutt, na daga cikin jarumai maza da suke da saurin kuka ko a gaban waye.

Da yake mahaifiyarsa ta jima da rasuwa, idan ya tunata a wasu lokuta za a ga yana zubar da hawaye.

Haka a lokacin da aka yanke masa hukuncin zaman gidan kaso na tsawon shekara biyar a 1993, Sanjay Dutt, har yanke jiki ya yi ya fadi kasa yana kuka a gaban bayyanar jama'a.

No comments