Breaking News

Ko sabbin manufofin Buhari za su dace da na masoyansa?Za a sake rantsar da Shugaba Buhari ne a karshen watan Mayun bana
Shugaba Muhammadu ya kasance shi kadai kuma na uku a jerin shugabannin kasar nan da ke kan mulki tun daga shekarar 1999 da ya lashe zabe.

Shi ne na biyu a cikin shekara 20 da ya lashe zaben sake kama ragamar mulki a karo na biyu, inda zai shafe tsawon lokaci zuwa shekara ta 2023 a kan mulki.

Tashin farko, an dan yi tababa a tsakanin masu sharhin warware badakalar siyasa kan cewa Buhari zai sake samun damar jan ragamar kasa a karo na biyu.

Kodayake gwamnatinsa ta yi fama da dimbin matsaloli tun daga shekarar 2015, kama daga kan zargin sako-sako da ya yi wajen tunkarar abin kunyar da wasu daga cikin manyan mataimakansa suka tafka.

Buhari a kashin kansa babu wani abin kunyar da yake tattare da shi, don haka har yanzu soyayyarsa ta shahara, musamman a arewa.

Sai dai ya kara kimar darajarsa akan abokin karawarsa na jam'iyyar PDP da karin kuri'u miliyan hudu, fiye da kuri'u miliyan biyu da rabi da ya dara Shugaban kasa Goodluck Jonathan a shekarar 2015.

Dan takarar jam'iyyar PDP, tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar, ya samu kuri'u miliyan 11 da dubu 300.

Wannan na nuni da kuri'u miliyan guda da rabi kasa da abin da PDP ta samu a shekarar 2015.

Raguwar masu kada kuri'a
Al'amari mafi muhimmanci da za a fahimta, shi ne daukacin 'yan takarar adadin kuri'unsu ya yi kasa bisa la'akari da abin da jam'iyyunsu suka samu, duk da cewa yawan masu kada kuri'a sun karu daga miliyan 69 a shekarar 2015 zuwa miliyan 84 a bana.

Ko mene ne ya haifar da hakan? Akwai akalla dalilai hudu.

Na farko dai shi ne daukacin 'yan takarar sun fito ne daga yankin arewacin, 'yan kabilar Fulani kuma Musulmi ne.

Wannan ya taimaka wajen rage tashintashina a fadin kasar, saannan ya sanya wasu masu kada kuri'a a daukacin fadin kudu da Arewa suka ji cewa ba su damu ba, ko ma wane ne ya samu nasarar lashe zaben.


Na biyu kuwa, karancin kudin da aka yi amfani da su a hada-hadar zabe in an kwatanta da zabukan Najeriya wadanda suka gabata.

Sabanin shekarar 2015 lokacin da jam'iyya mai mulki ta PDP aka ce ta kashe biliyoyin daloli a wajen yakin neman zabe.

Wannan karon kuwa Buhari mutum mai tsauri da matse hannu (tsuke bakin aljihu).

Sai da ya tabbatar da cewa APC na da karancin kudin da za ta aiwatar da yakin neman zaben wannan shekarar.

Ita ma jam'iyyar PDP ba ta da isassun kudi in an kwatanta da abin da take da shi a shekarar 2015.

Kuma jita-jitar da aka baza cewa Atiku zai kwararo kudi a cikin kasar lamarin dai bai tabbata ba.

Masu yin zabe sun fahimci cewa akwai karancin manyan hotuna da ake likawa a bango da alluna da tallace-tallace 'yan takara a rediyo da talabijin da jaridu da kyautar kudin da 'yan siyasa ke rabawa.

Dalili na uku, shi ne daukacin 'yan takarar a wannan zaben sun yi yakin neman zabe ne na wani takaitaccen lokaci.

Duk da cewa dokar zabe ta lamunce a yi watanni uku ana gudanar da yakin neman zaben, daukacin Buhari da Atiku sun kewaya kasar nan ne a cikin watan da ya wuce, inda suka gudanar da manyan taruka.

Sannan kuma dage zabe da aka yi a makon da ya wuce ya haifar da karanci masu fitowa zabe.

Mafi yawancin mutanen da suka yi tafiya zuwa garuruwansu don kada kuri'a a makon da ya wuce, sun kasa sake yin tafiya a karshen wannan mako

Shugaba Buhari ya samu nasarar lashe zabe a jihohi 19, yayin da Atiku ya samu nasarar a jihohi 17, tare da babban birnin Tarayya Abuja.


Farfesa Mahmoud Yakubu ya mika wa Muhammadu Buhari shaidar lashe zaben a ranar Laraba
Jihohin da Buhari ya lashe zabe su ne Legas da Ogun da Ekiti da Osun da Kwara da Kogi da Nasarawa da Kaduna da Neja da Zamfara da Sakkwato da Kebbi da Katsina da Kano da Jigawa da Yobe da Borno da Gombe da kuma Bauchi.

Atiku ya ci zabensa a Oyo da Ondo da Edo da Delta da Bayelsa da Ribas da Akwa Ibom da Kuros Riba da Abiya da Imo da Anambra da Enugu da Ebonyi da Binuwai da Taraba da Adamawa da Filato da Babban birnin Tarayya FCT.

Jihohi biyar ne kadai suka sauya bangare tun daga shekarar 2015.

Yayin da jihar Ekiti, wadda ke goyon bayan PDP a shekarar 2015 yanzu ta zabi APC, Binuwai da Adamawa da Oyo da Ondo jihohin da suka goyi bayan APC a shekarar 2015 yanzu sun zabi PDP.

Baya ga haka, daukacin jihohin da Babban birnin Tarayya sun yi zabe ne kan turbar salon da suka yi a shekarar 2015.

Buhari ya samu nasarar lashe wannan zaben ne saboda dimbin goyon bayan da ya samu daga yankin arewa.

Ya samu miliyoyin kuri'u daga jihohin Kano da Katsina da Kaduna da Barno da Bauchi da kuma Jigawa.

Sannan ya samu dimbin kuri'u daga Sakkwato da Kebbi da Neja da Gombe da Yobe da kuma Nasarawa.


Wani magoyin bayan Shugaba Buhari a jihar Adamawa bayan sanar da sakamakon zaben
Duk da haka ya yi asarar kuri'u kimanin rabin miliyan a jihar Kano kawai, in an kwatanta da abin da ya samu a shekarar 2015.

Yayin da Buhari ya samu lashe zabe a daukacin yankin Kudu maso Yamma ban da Ekiti a shekarar 2015, a wannan karon kuwa ya fadi zabe a muhimman jihohin Yarbawa biyu, wato Oyo da Ondo.

Dimbin kuri'un da ya samu a jihar Legas mai yawan al'umma su ma sun ragu in an kwatanta da abin da ya samu a shekarar 2015.


'Yan Najeriya da dama ne suka nuna murna ta hanyoyi daban-daban bayan da aka sanar da Shugaba Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben
Shugaba Buhari bai samu komai ba a yankin Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu, wadannan ne dai wuraren da ba su zabe shi a shekarar 2015.

Bai samu nasarar lashe zabe a jiha guda da ke yankuna biyu, wadanda suka hada da Imo da Edo, wadanda ke karkashin ikon mulkin jam'iyyarsa ta APC.

Abu mafi muhimmanci a yanzu, shi ne Buhari ya sake lashe zabe.

Kodayake abokin hamayyarsa Atiku ya ki amincewa da sakamakon, kuma yana shirin kalubalantarsa a kotu.

Ya yi zargin cewa an yi magudin zabe da yawa a wuraren da yake da karfin tasiri.

Don haka a wannan shekarar ba za mu samu jin mashahuriyar wayar tarhon nan da muka ji irinta ba a shekarar 2015, lokacin da Shugaba Jonathan ya amince da faduwarsa zabe.

Abin da ya rage yanzu, shi ne Buhari ya baje tsare-tsaren ayyukan da yake nufin aiwatarwa a wa'adin mulkinsa karo na biyu, kuma na karshe.

Shin ko manufarsa da tsarin ayyukansa za su sha bamban da abin da 'yan Najeriya suka gani a zamanin mulkinsa karo na farko, lokaci ne kawai zai tabbatar da hakan.

 Daga Mahmud Jega, mai sharhi kan al'amuran siyasar Najeriya

No comments