Kun taba ganin yadda ake tseren karnuka? - DWGUNSAU'S BLOG

Breaking

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Monday, 4 March 2019

Kun taba ganin yadda ake tseren karnuka?
Jama'a da dama sun taru a birnin Anchorage dake Alaska a ranar Asabar domin murnar fara gasar tseren karnuka ta 'Iditrod' karo na 47 da ake yi a yanayin kankara.


Tseren ya bambanta da na dawaki ko hawan rakumi inda mutane ke hawa saman dabbobin, a nan karnukan ne ke jan mutum cikin wani abu mai kamar amalanke a lokaci tseren.

Tawagar mutanen da karnukan ke ja a lokacin tseren kenan inda suke shirye-shiryen tseren da ke shafe kusan kilomita 1,600.

Akan yi tseren ne daga Willow zuwa Nome duk dake yankin Alaska.


Gasar da za a fara a ranar Lahadi, tawagar karnuka 14 ne za su shiga gasar, inda ake sa ran za su tsallake tsaunuka biyu duka masu matsananciyar dusar kankara.


An samu takaddama a gasar a 'yan shekarun da suka gabata sakamakon matsalar yaudara da aka samu na ba wasu karnuka kwayoyi ba bisa ka'ida ba domin cin gasar wanda hakan ya yi sanadiyar wasu manyan masu daukar nauyin gasar suka zame hannuwansu daga gasar.


Cikin masu tseren, kowane daga cikinsu zai tanaji karnuka 16 wadanda ake kira da 'Alaskan Hukkies', amma a dokar gasar karnuka biyar ne kacal za a iya karasa gasar da su.

Gasar na karkarewa ne idan aka iso garin Nome bayan an shafe tafiya mai tsawo daga Willow.

Karnukan da suka samu raunuka a lokacin tseren ko kuma rashin lafiya ta kamasu, akan ajiye su a wasu zabbabun wurare da aka kebe a kan hanyar da tseren ke gudana.

An yi haka ne domin idan irin wannan matsalar ta taso a kula da karnunkan inda daga baya ake daukar karnukan a kai su garin Nome sai masu su su karba daga baya.

Bincike ya nuna cewa sama da karnuka 150 ne suka mutu a wannan gasar tun da aka fara a 1973.


An kawo manyan motoci cike da dusar kankara inda aka baje dusar a kan tituna na garin Anchorage domin shirye-shiryen fara gasar.


A bara, Joar Leifseth Ulsom wanda dan asalin kasar Norway ne ya lashe gasar inda ya kwashe kwanaki tara da sa'oi' 12 tare da karnukansa suna gudu.

Mista Joar ya samu kyautar dala dubu 50 a matsayin kyautar lashe gasar.


Mista Joar ne na farko dan wata kasa daban da ya lashe gasar bayan wasu Amurkawa 'yan gida daya sun shafe shekaru 7 suna lashe gasar.

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad

Responsive Ads Here