Breaking News

Peter Tabichi: Malamin makarantar da ya ci kyautar naira miliyan 360

Peter Tabichi: Malamin makarantar da ya ci kyautar naira miliyan 360

Peter Tabichi
Wani malamin makaranta a kauyen Kenya da ya saba bayar da akasarin albashinsa domin taimaka wa dalibai marasa galiho ya samu nasarar lashe kyautar gwarzon malami na duniya.

Peter Tabichi ya samu dala miliyan 1, wato kimanin kudin Najeriya naira miliyan 360 ke nan.

Malamin ya samu yabo wajen taimaka wa wata makaranta mai karancin azuzuwa da yawan dalibai.

Mista Peter wanda yake koyar da darasin kimiyya ya ce yana so dalibai su nakalci kimiyya domin kawo ci gaba a rayuwar gobe.

An bayyana malamin wanda aka bashi kyautar a birnin Dubai na kasar Haddadiyar Daular Larabawa a matsayin wanda yayi fice wajen taimaka wa dalibai da suke a karkara a kasar Kenya.

Malamin na bayar da kashi 80 cikin 100 na albashinsa ne ga dalibansa.


Habbaka kimiyya

Daliban da Mista Peter yake taimakamawa akasarinsu marayu ne ko kuma sun fito daga gidajen marasa galihu.

Malamin ya ce yana so ne ya kara cusa soyayyar darasin kimiyya da kuma kara kawo ci gaba a fannin kimiyya ba wai a kasar Kenya kawai ba, amma har a nahiyar Afirka.

Bayan ya lashe wannan kyautar, malamin ya yaba da kwazon matasan Afirka.

Ya ce "a matsayina na malamin kimiyya da nake tare da dalibai kullum, ina ganin yara masu kwazo da fasaha da kuma bai wa iri-iri.''

''Ina sa ran cewa Afirka za ta samar da masana kimiyya da injiniyoyi da kuma manyan 'yan kasuwa wadanda za a san da su a fadin duniya, kuma yara mata za su kasance a cikin su.

Dalibai da dama suna tafiyar kusan kilomita shida, kafin su isa makarantaAikin koyarwa

Mista Peter ya ce irin kalubalen da yake fuskanta a matsayin malami shi ne irin kokarin da yake yi domin wayar da kan mutanen karkara kan muhimmancin ilimi da kuma kai ziyara ga iyayen yaran da akwai barazanar yiwuwar cire su daga makaranta.

Mista Peter yana kokarin sauya ra'ayin iyayen da suke kokarin aurar da 'ya'yansu da wuri inda yake ba su shawarar su bar 'ya'yansu mata su yi karatu.

Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ya taya malamin murna kan kyautar

Mista Peter ya ce wannan kyautar da ya samu ta nuna cewa yana kan hanya madaidaiciya.

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya taya malamin murna kan kyautar da ya samu.

Ana bayar da wannan kyautar ne a duk shekara domin kara daraja sana'ar malanta


No comments