Breaking News

Real Madrid ta dauki Eder Militao

Real Madrid ta dauki Eder MilitaoKungiyar Real Madrid, ta dauki mai tsaron baya na kulob din FC Porto, Eder Militao.

Dan wasan mai shekara 21, shi ne na farko da Zinedine Zidane ya saya, bayan da ya sake karbar aikin kocin Madrid.

A sanarwar da Real ta sanar a shafinta na Intanet ta ce ''Real Madrid ta cimma yarjejeniya daukar dan wasan FC Porto, Eder Militao''.

Dan kwallon na Brazil ya amince zai koma Spaniya kan shekara shida, zai kuma koma can ne idan an kammala wasannin bana.

Rahotanni na cewa kudin daukar dan kwallon Brazil din ya kai fam miliyan 43.5, ana sa ran yarjejeniyarsa da Real za ta kare a karshen watan Yunin 2025.

Militao ya fara buga tamaula a Sao Paulo daga nan ya koma FC Porto a watan Agustan 2018, ya kuma taimakawa kungiyar Portugal ta kai wasan daf da na kusa da na karshe a gasar Zakarun Turai ta bana.

Tuni aka fitar da Real Madrid a gasar kofin Zakarun Turai da kuma Copa del Rey, sannan tana ta uku a kan teburin La Liga da tazarar maki 12 tsakaninta da Barcelona ta daya.

No comments