Breaking News

Sheikh Ahmad Sulaiman ya kubuta daga hannun masu garkuwa

                              Sheikh Ahmad Sulaiman ya kubuta daga hannun masu garkuwa


Masu garkuwa da mutane sun sako mahaddaccin kur`ani Sheikh Ahmad Sulaiman .

Daya daga cikin iyalan Sheikh Ahmad, Malam Muhammad Kabir, ya bayyanawa wakilinmu cewa, Sheikh Ahmad Sulaiman yana nan cikin lafiya kuma yana hanyarsa ta zuwa garin Kano, sun godewa Allah da Ya kubutar da shi daga hannun masu garkuwa da mutane.

An yi garkuwa da Sheikh Sulaiman da wasu mutum biyar, sun yi kwanaki 13 a hannun masu garkuwan a hanyar Sheme zuwa Kankara jihar Katsina.

1 comment: