Breaking News

Shugaban Aljeriya ya hakura da tazarcen karo na biyar

Shugaban Aljeriya ya hakura da tazarcen karo na biyar

Abdelaziz Bouteflika, a wani hoton da aka dauke shi a 2017

Shugaban kasar Aljeriya Abdelaziz Bouteflika ya dage zaben kasar da za a yi ranar 18 ga watan Afrilu, kuma ya ce ba zai tsaya takarar neman tazarce karo na biyar ba.

Takarar Shugaba Bouteflika ta janyo zanga-zanga sosai a fadin kasar a makon da ya gabata.

Kimanin shekara 20 ke nan yana mulkin kasar Aljeriya, amma ba a cika ganinsa ba tun da ya samu shanyewar jiki a 2013.

Sanarwar ta zo ne bayan kwana daya da dawowarsa, mai shekara 82 ya dawo gida ne daga wani asbibiti dake kasar Switzerland inda ya kwashe makonni biyu a can.


"Ba zan yi mulki karo na biyar ba," a cewar shugaban a wata sanarwar manema labarai da aka fitar a ranar Litinin.

"Da ma ban sanya a rai ba. Bisa la'akari da yanayin lafiyata da shekaruna, hidimar karshena ga mutanen Aljeriya ita ce tabbatar da gina ingantaccen tushen sabuwar jamhuriyya."

A makon da ya gabata, ya sha alwashin sauka daga mulki da wuri idan ya ci zabe, amma hakan bai gamsar da dubban mutanen kasar ba masu zanga-zanga.An kara sanya matsi ga Bouteflika bayan da sama da Alkalai 1000 a ranar Litinin suka bayyana cewa ba za su yi hukunci a kan zaben ba idan yana takara.

Sannan kuma shugaban Hafsin sojojin kasar gaba daya, Janar Gaed Salah ya bayyana cewa da sojojin kasar da jama'ar kasar sun yi wani tanadi sosai domin rayuwar a gaba.

Wata majiya ta nuna cewa sojojin kasar na goyon bayan zanga-zangar kasar.

Manyan malaman kasar sun yi Allah-wadai da yunkurin tilasta su su yi huduba a kan goyon bayan gwamnati.

"Ku bar mu mu yi aikinmu, kada ku sanya mana baki" a cewar Imam Djamel Ghoul, wani babban malami marar darika a kasar.
Algeria ta fuskanci zanga-zanga daban-daban inda dalibai da malamai suka yi yajin aiki, haka zalika masu shaguna da jiragen kasa su ma suka bi sahunsu.

Shugaba Bouteflika ba a ganinsa a kasar. Fitowarsa ta karshe a bainar jama'a ita ce wadda ya yi a 2014 bayan da ya lashe zaben da aka yi.

'Yan Algeria da yawa na nuna damuwa a kan rashin lafiyarsa da kuma yawan shkearunsa, inda wasu ke jin tsoron mutuwarsa a kan mulki za ta iya kawo rudanin siyasa a kasar.

No comments