Breaking News

Tarihin hatsarin jiragen sama da aka taba yi a duniya

  Tartibin hadurran jiragen sama tun daga 1998 zuwa 2018


Ranar 29 ga Oktoba jirgin sama kirar Boeing 737 Max, mallakar kamfanin sufurin jiragen sama na Lion Air ya yi hadari da shi a tekun Java jim kadan bayan tashinsa daga birnin Jakarta na kasar Indonesiya.

Daukacin fasinjoji 189 da matukan jirgin duk sun mutu, kuma wani mai aikin ceton sa-kai da ke iyo a ruwa shi ma ya halaka.

Masu bincike sun ce (jirgin) na da matsala a cikin injinsa, wanda kamata ya yi a dakatar da tashinsa (hada-hadar sufurinsa har sai an shawo kan matsalarsa).

18 ga Mayu: Jirgi kirar Boeing 737 mai daukar fasinjoji ya yi hadari, inda ya rikito jim kadam da dagawarsa daga baban filin tashin jiragen sama na Jose Marti da ke Havana (kasar Cuba), inda ya halaka mutane 112.

11 ga Afirilu: Jirgin sama ya yi hadari jim kadan da dagawarsa sama a kusa da babban birnin Aljeriya na Aljiers, wanda ya halaka daukacin fasinjoji 257, wadanda suka hada da matukansa 10. Mafi yawan wadanda suka mutu sojoji ne da iyalnsu.

12 ga Maris: Wani jirgin saman daukar fasinjoji 71 da matukansa ya yi hadari wajen saukarsa a filin jirgin sama Kathmandu (kasar Nepal). Mutane sama 50 ne suka mutu lokacin da jirgin kirar Bombadier Dash 8 turboprop ya dumfari taba kasa.

18 ga Fabriru: Wani jirgin fasinjoji ya yi hadari a tsaunukan Zagros da ke Kasar Iran, inda daukacin fasinjoji 66 suka halaka. Jirgin mallakar kamfanin sufuri na Aseman Max Airlines ATR Jirgin kirar 'turboprop' ya yi hadari, inda kimanin sa'a guda bayan tashinsa daga baban birnin kasar, Tehran lokacin da ya nufi birni da ke Kudu maso yammacin kasar, Yasuj.

11 ga Fabrairu: Wani jirgin fasinjan Rasha ya yi hadari mintuna kadan da tashinsa daga filin jirgin saman Domodedovo da ke Mosko tare da fasinjoji 71, jirgin kirar Antonovo An-148, mallakar kamfanin sufuri na Orsk a tsaunukan Ural, lokacin day a yi hadari a kauyen Argunovo, kimanin kilomita 80 (mil 50) da ke Kudu maso Gabashin Mosoko.

2017
Ba a samu hadrin jirgin sama a shekarar 2017 - wato wannan shekara ce da ta kasance mai kariyar aukuwar hadarin jiragen sufurin saman a tarihi.

2016
25 ga Disamba: Wani jirgin saman sojan Rasha kirar Tu-154 jet Ailiner ya yi hadari a tekun Black Sea, inda aka samu asarar rayuka 92 tare da matukan jirgin.

Jirgin ya rikito ne kasa jim kadan da tashinsa sama a wani filin jirgin sama da ke kusa da birnin Sochi. Jirgin na dauke ne a 'yan wasa wanda aka shirya za su yi wa rundunar sojan Rasha da ke Siriya kade-kade da raye-raye, tare da ''yan jarida da sojoji.


Jirgin na dauke ne a 'yan wasa wanda aka shirya za su yi wa rundunar sojan Rasha da ke Siriya kade-kade da raye-raye, tare da ''yan jarida da sojoji
7 ga Disamba: Daukacin mutane 48 da ke cikin jirgin fasinjan kasar Pakistan na PIA sun halaka lokacin da jirgin ya yi hadari a Arewacin kasar.

Jirgin mallakar kasar tuni daman an yi fama da shi kan kin tabbatar da matakan kariya - inda daga bisani aka jajirce kan cewa sai an binciki jirgi mai lamba PK-661 wanda ya taso daga Chitral zuwa Islamabad ba, wanda ba a same shi da nuna wata alama ta matsalar inji a tattare da shi ba.


Daukacin mutane 48 da ke cikin jirgin fasinjan kasar Pakistan na PIA sun halaka lokacin da jirgin ya yi hadari a Arewacin kasar
28ga Nuwamba: Jirgin da ke dauke da kungiyar 'yan kwallon kafar Brazil kulo din Chapecoen mai ya kare masa, inda ya rikito a Medelin da ke Colombia ya halaka mutane 71,. wadanda suka hada da ''yan wasa da jami'an gudanar da kulob din. sai dai ''yan wasa uku na cikin wadanda suka tsira mutum shida, yayin da wasu mutane tara (daga cikin''yan wasan) kuwa daman ba su samu yin tafiyar ba.

19 ga Mayu:Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya tabbatar da hadarin jirgin saman Masar Egypt Air, wanda aka bayar da rahoton bacewarsa a tsakanin Parsi da Cairo, inda ya yi hadari ya halaka mutane 66 da ke cikinsa.

19 ga Maris: Wani jirgin FlyDubai kirar Boeing 737-800 ya yi hadari a Rostov-on-Don da ke kasar Rasha, inda ya halaka daukacin mutane 62 da ke cikinsa.

2015
31 ga Oktoba: Wani jirgi kirar An AirbusA321 mallakar kamfanin sufurin jiragen saman Rasha Kogalymav ya yi hadari inda ya rikito adaga saman tsaunin Sinai da kimanin mintuna 22 da dagawarsa sama bayan tasowarsa daga Sharm el-Sheikh, inda ya halaka daukacin mutane 224 da ke cikinsa. Kungiyar fafutikar Musulunci ta da ke yankin ta yi ikirarin kado da jirgin don daukar fansa kan daukin da Rasha ta kai kasar Siriya.

30 ga Yuni: Jirgin saman sojan Indonesiya kirar Hercules C-130 na sufuri ya yi hadari a wata unguwa d aMedan. Jami'an soja sun ce daukacin mutane 122 da ke cikin jirgin duk sun mutu, tare da wasu mutane 19 da hadarin ya rutsa da su a kasa.

24 ga Maris: Jirgin sama kirar Germanwings Airbus A320 ya yi hadari a tsaunukan Alps kusa da Digne lokacin da ya tashi daga Barcelona zuwa Dusse. Daukacin mutane 148 da ke cikin jirgin an shiga fargabar mutuwarsu.

2014
28 ga Disambar: Jirgin sama kirar AirAsia QZ8501 da ya taso daga Surabaya da ke kasar Indonesiya zuwa Singapore ya bace a tekun Java. matukin jirgin ya yiwo wayar neman izinin karkata akalar tafiyar jirgin bisa dalilan munin yanayi, amma bai samu amsa ba. a cikinsa akwai fasinjoji 162 tare da masu aikin kula da su.

24 ga Yulin: Jirgin saman kasar Aljeriya na Air Algerie mai lamba AH5017 ya bace a sararin samaniyar kasar Mali daidai lokacin da aka yi fama da munin yanayi a kan iyakar kasar da Burkina Faso jirgin kirar e McDonnell Douglas MD-8 mallakar kamfanin kasar Spain ne na Swiftair, sannan ya hjnufin birnin Ouagadougou daga Algiers dauke da fasinjoji 116, 51 daga cikinsu Faransawa ne. Daukacinsu dai duk an kaddara mutuwarsu.

23 gaYuli: Mutum 48 sun mutu lokacin da wani jirgin saman kasar Taiwan na Taiwanese ATR-72 ya yi hadari a wani teku da ya yi toroko lokacin da jirgin ya tashi ba da dadewa ba.

Shi ma wani jirgin TransAsia Airways GE222 dauke da fasinjoji 54 da masu kula da fasinjoji hudu da suka nufi tsibirin Penghu. Ya yi yunkurin karkatar da akalarsa daga sauka kasa kafin ya yi hadari dakika guda da yunkurin.


Jirgin sama mallakar kasar Malesiya na MH17 ya yi hadari a kusa da garin Grabove da ke gabashin kasar Ukraine, ind aya halaka daukacin mutane 298 da ke cikinsa
17 ga Yuli: Jirgin sama mallakar kasar Malesiya na MH17 ya yi hadari a kusa da garin Grabove da ke gabashin kasar Ukraine, ind aya halaka daukacin mutane 298 da ke cikinsa, kuma mutane 193 daga cikin ;'yan tawagen Dutc ne da ke goyon bayan Rasha wadanda aka zarge su da harbin jirgin suka kakkabo shi kasa, ta hanyar amfani da makami mai linzami, sai dia sun musanta aikat ahakan.

8 ga Maris: Jirgin sufurin saman kasar Malesiya na MH370 wanda ya tashi daga birnin Kuala Lumpur zuwa Beijing ya bace, al'amarin da ya haifar da bazama nemansa ka'in da na'in wanda ba a taba yin irinsa ba a tsawon tarihi hada-hadar sufurin jiragen sama.. Duk da irin dimbin kokarin da aka yi, musamman a yanki mai mawuyacin hali na Kudancin tekun Indiya, babu abin da aka gano har zuwa yulin 2015, yayin da da ruwa ya turo fuffuken jirgin waje a kan tsibirin Reunion. Jami'an gwamnatin Faransa sun tabbatar da cewa an samu buraguzan jirgin MH370 (da ya yi batan dabo).

11 ga Fabrairu: Wani jirgin daukar kaya na soja samfurin a Hercules C-1 dauke da mutajne 78 ya yi hadari a wani yankin tsaunukan Arewa maso Gabashin Aljeriya. Rahotanni sun nuna cewea mutum daya ne ya tsira daga jami'an sojan, daga iyalan soja da matukan jirgin.

2013
17 ga Nuwamba: Jirgin Kamfanin sufurin jiragen sama na Tatarstan kirar Boeing 737 ya yi hadari lokacin saukarsa a Kazan da ke kasar Rasha, inda ya halaka daukacin mutane 50 da ke cikinsa.

16 ga Oktoba: Mutane arba'in da tara, wadanda suka hada da 'yan kasar waje da suka fito da kimanin kasashe 10, tare da 'yan kasar Laotian, sun mutu ya yin da jirgin sufurin saman Lao Airlines aTR 72-600 ya tsunduma cikin kogin Mekong lokacin da ya yi yunkurin sauka.

2012
3 ga Yuni: Jirgin sufuri na Dana Air dauke da fasinjoji 150 ya yi hadari a wani yanki da ke cunkushe da jama na birni mafi girma a Najeriya, wato Legas.

20 ga Afirilu:Wani jirgin saman A Bhoja Air kirar Boeing 737 ya yi hadari lokacin da ya kusa isa filin jiragen saman babban birnin Pakistan Islamabad, inda ya halaka daukacin fasinjoji 121 da matukansa su shida.

2011
26 ga Yuli: Wasu mutane 78 sun halaka a hadrin jirgin saman sojan kasar Moroko kirar C-130 Hercules wanda ya yi hadari a tsaunin da ke kusa da Guelmin da ke kasar Moroko. Jami'an Gwamnatin Moroko sun dora alhakin aukuwar hadar kan mummunan yanayi.Matukan jirgin sun kai rahoto matsalatr inji kafin sun yi yunkurin sauka kasa
8 ga Yuli: Jirgin sufurin sama na Hewa Bora Airwa ya yi hadari sanadiyyar mumunan yanayi a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, inda mutane 74 suka halaka daga cikin mutane 118 da ke cikin jirgin.

9 ga Janairu: Jirgin sufurin saman kasar Iran IranAir kirar Boeing 727 ya babbale gutsi-gutsi a kusa da birnin Orumiyeh, inda mutane 77 suka mutu daga cikin mutane 100 da ke cikin jirgin.

Matukan jirgin sun kai rahoto matsalatr inji kafin sun yi yunkurin sauka kasa.

2010
5 ga Nuwamba: Jirgin fasinjan Aerocaribbean kirar turboprop ya yi hadari a tsaunukan da ke tsakiyar kasar Cuba, inda daukacin mutane 68 da ke cikin jirgin suka mutu.

28 ga Yuli: Jirgin saman hada-hadar sufurin cikin gida na kasar Pakistan Airblue da ya taso daga birnin Karachi ya yi hadari a wani gabar dutse yayin da ya yi yunkurin sauka a filin jiragen saman Islamabad, inda ya halaka daukacin mutane 152 da ke cikinsa.

22 ga Mayu: Jirgin saman sufurin kasar Indiya na Air India Express Boeing 737 yyin da ya haure saman wani dutse a filin jirgin saman Manglore da ke kudnacin Indiya, sai ya yi hadari a gabar wani dutse, inda ya kama da wuta , inda ya halaka mutun 158.

12 ga Mayu: Jirgin saman sufuri na kasar Libiya Afriqiyah Airways kirar Airbus 330 yayin da ya yi yunkurin sauka afilin jirgin saman Tripoli da ke kasar Libiya, ind aya halaka sama da mutum 100.

10 ga Afirilu: Wani jirgi kirar Tupolev 154 dauke shugaban kasar Poland Lech Kaczynski ya yi hadari a kusa da filin jiragen saman Rasha na Smolensk, inda sama da mutane 90 da ke cikinsa suka mutu.

25 ga Janairu: Jirgin sufurin saman kasar Habasha mai duakar fasinjoji na Ethiopian Airlines ya afka cikin teku tare da mutane 89 da ke cikinsa jim kadan da tasowarsa daga birnin Beirut (na kasr Lebanon)

2009
15 ga Yuli: Jirgin saman sufurin Caspian Airlines samfurin Tupole ya yi hadari a Arewacin kasar Iran yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Armenia. Daukacin fasinjoji 168 da matukansa an bayar da rahoton mutuwarsu.

30 ga Yuni: jirgin saman safar fasinja na kasar Yemen kirar Airbus 310 ya yi hadari inda ya afka tekun Indiya kusa da tsaunukan Comoros archipelago. mutum daya ne daga cikin mutane 153 da ke cikin jirgin ya tsira.

1 ga Yuni: Jirgin sufurin saman Faransa kirar Airbus 330 da ya taso daga birnin Rio de Janeiro zuwa Paris ya yi hadari inda ya afka tekun Atlantic tare da mutane 228 da ke cikinsa. Daga bisani masu aikin ceto sun lalubo gawarwakin mutane 50 a cikin tekun.Jirgin saman sojan kasar Indonesiya kirar C-130 Hercules mai dakon kaya ya yi hadari a kauyen da ke gabashin Java, inda akala mutane 97 suka halaka.
20 ga Mayu: Jirgin saman sojan kasar Indonesiya kirar C-130 Hercules mai dakon kaya ya yi hadari a kauyen da ke gabashin Java, inda akala mutane 97 suka halaka.

12 ga Fabrairu:Jirgin fasinja ya yi hadari a wnai gida da ke Buffalo, a birnin New York (da ke kasar Amurka), inda dukacin mutane 49 da ke cikinsa da wani mutum guda da hadarin jirgin ya rutsa da shi a kasa har ya mutu.

2008

14 ga Satumba: Wani jirgi kirar Boeing-737 da ya yi hadari lokacin saukarsa a kusa da wani birni na Perm da ke tsakiyar kasar Rasha, inda ya halaka daukacin fasinjoji 88 da matukansa da ke ciki.

24 ga Agusta: Wani jirgin fasinja ya yi hadari jim kadan da tashinsa daga Bishkek babban birnin Kyrgyzstan, inda ya halaka mutane 68.

20 ga Agusta: Jirgin saman ksar Spain ya karkace wa titin yunkurin tashin jiragen sama a filin jiragen saman Madrid Barajas, inda ya halaka mutane 154, tare da jikkata wasu mutane 18 da suka samu raunuka.

2007

30 ga Nuwamba: Daukacin mutane 56 da ke cikin hjirgin saman Atlasjet sun mutu lokacin da jirgin ya yi hadari a kusa da garin Keciborlu a yankin tsaunukan Lardin Isparta, da ke kimanin kilomita 12 (mil 7.5) daga filin jiragen saman Isparta.

16 ga Satumba: Akalla mutane 87 suka mutu yayin da wani jirgin sama ya yi wata irin saukar harigido a cikin mummunan yanayi a wajen shakatawa na Thailanda da ke Phuket.

17 ga Yuli: Wani jirgin saman sufuri na kamfani TAM Airline ya yi hadari a wajen saukarsa a filin jiragen saman Congonhas da ke Sao Paulo a kasar Brazil, al'amarin da ya kasance mummunan hadarin jirgin saman da ba a taba yin irinsa ba. Mutane 199 suka mutu - daukacin mutane 186 da wasu mutane 13 da hadarin ya rutsa da su a kasa.

5 ga Mayu: Jirgin kamfanin sufurin saman kasar Kenya kirar Boeing 737-800 ya yi hadari a harkakiyar ciyayin tabo da ke kudancin kasar Kamaru, inda daukacin mutane 114 da ke cikinsa suka mutu. Binciken da jami'ai suka gudanar har yanzu bai bayar da musababbin hadarin ba.

1 ga Janairu: Wani jirgin sufurin saman Adam Air kirar Boeing 737-400 dauke da fasinjoji 102 da matukansa ya fado kan tsaunukan da ke tsibirin Sulawesi a sufurin cikin gida da ya gudanar a kasar Indonesiya. Daukacin wadanda ke cikin jirgin duk sun mutu.

2006

29 ga Satumba: Wani jirgi kirar Boeing 737 dauke da fasinjoji 154 tare da matukansa y yi hadari a dajin Amazon da ke kasar Brazil, inda dukacin mutanen da ke cikins asuka mutu, bayan da ya yi karo da wani babban jirgi a tsakiyar sararin samaniya.

22 ga Agusta: Wani jirgin kasar Rasha kirar Tupolev-154 dauke da fasinjoji 170 ya yi hadari a Arewacin Donetsk da ke gabashin Ukrain.

9 ga Yuli: Wani jirgin kasar Rasha samfurin Russian S7 kirar Airbus A-31 ya sauka daga titin tashin jiragen sama lokacin da ya sauka a filin jiragen saman Irkutsk da ke Siberia. Kimanin mutane 124 da ke cikin jirgin sun mutu, amma fiye da mutum 50 sun tsira.

3 ga Mayu: Wani jirgin Armavia kirar Airbus A-320 ya yi hadari a tekun Black Sea kusa da Sochi, inda daukacin mutane 113 da ke cikinsa suka mutu.

2005

10 ga Disamba: Wani jirgin sufuri na Sosoliso Airlines DC-9 ya yi hadari a birnin Fatakwal da ke Kudancin Najeriya, inda ya halaka mutane 103 da ke cikinsa.

6 ga Disamba: Wani jirgin soja kirar AC-130 na sufuri ya yi hadari a wajen babban birnin kasar Iran, Tehran, inda mutane 110 da ke cikinsa, tare da wasu da hadarin ya rutsa da su a kasa.Wani jirgin sufuri na Mandala Airlines dauke da fasinjoji 112 da matukansa mutum biyar ya yi hadari bayan tashinsa daga birnin Medan da ke kasar Indonesiya
22 ga Oktoba: Wani jirgin sufuri na Bellview airlines kirar Boeing 737 dauke da mutane 117 da ke cikinsa ya yi hadari bayan tashinsa daga birnin Legas da ke Najeriya, inda ya halaka duk wanda ke cikinsa.

5 ga Satumba: Wani jirgin sufuri na Mandala Airlines dauke da fasinjoji 112 da matukansa mutum biyar ya yi hadari bayan tashinsa daga birnin Medan da ke kasar Indonesiya, inda ya halaka daukacin mutanen da ke cikinsa, tare da wasu da hadarin ya rutsa da su a kasa.

16 ga Agusta: Wani jirgin kasar Columbia na kamfanin sufurin West Caribbean Airways ya yi hadari a wata karkara da ke kasar venezuela, inda daukacin mutane 160 da ke cikinsa suka halaka. Jirgin wanda ya tunkari kasar Panama zuwa Martinique, an ajiye shi a wata unguwa da ke tsibirin Carribbean.

14 ga Agusta: Jirgin sufurin kamfanin Helios Airways ya taso daga Cyprus zuwa Athens dauke da mutane 121 ya yi hadari a Arewaci babban birnin kasar Girka, Athens, nan take bayan ya yi sako-sakon rashin karfin da ke rikonsa a sama.

16 ga Yuli: Jirgin sufuri na Equatair ya yi hadari nan take da tashinsa daga tsibirin babban birnin kasar Equatorial Guinea, Malabo, da ke Yammacin kasar, inda daukacin mutane 60 da ke ciki suka mutu.

3 ga Fabrairu: An gano buraguzan balgataccen jirgin Kam Air kirar Boeing 737 a manyan tsaunukan da ke kusa da birnin Kabul na kasar Afghanistan, kwanaki biyu bayan da jirgin ya bace wa na'urar bin kadin tafiyarsa a cikin yanayin zubar kankara. Daukacin mutane 104 da ke cikinsa an ce sun mutu.

2004

21 ga Nuwamba: Jirgin saman fasinja ya afka cikin tafkin kankara da ke kusa da birnin Bbaotou da ke can cikin yankin Mangolia da ke Arewacin kasar Sin, inda daukacin mutane 53 da ke cikin jirgin suka halaka, tare da wasu mutane biyu da hadarin ya rutsa da su, kamar yadda jami'an hukuma suka bayyana.

3 ga Janairu: Jirgin sufurin saman Masar mallakar kamfanin sufurin jiragen sama na Flash Airlines ya fada cikin tekun Red Sea, inda daukacin mutane 141 da ke cikinsa suka mutu. Mafi yawan fasinjojin ana da tabbacin ''yan yawon bude ido ne daga kasar Faransa.

2003

25 ga Disamba: Wani jirgi kirar Boeing 72 ya yi hadari daga tashinsa daga kasar Benin da ke yankin Afirka ta Yamma, inda ya halaka akalla mutane 135 da ke kan hanyarsu ta zuwa Lebanon.

8 ga Yuli: Wani jirgi kirar Boeing 72 ya yi hadari a Sudan jim kadan da tashinsa, inda ya halaka mutane 115 da ke cikinsa. Fasinja daya ne da wani jariri suka tsira.Hatsarin jirgi a Jamhuriyar Benin mai samfurin Boeing 727 ya fado jim kadan da tashinsa dropped out of the sky soon after take-off, killing at least 135 people travelling to Lebanon
26 ga Mayu: Jirgin saman Ukrainian Yak-42 ya yi hadari kusa da wurin shakatawa na tekun Black Sea na Trabzon da Arewa maso yammacin Turkiyya, inda ya halaka daukacin mutane 74 da ke cikinsa - kuma mafi yawancinsu masu aikin tabbatar da zaman lafiya da suka fito daga kasar Spain yayin da suke komowa gida daga kasar Afghanistan.

8 ga Mayu: Kimani mutane 170 ne aka bayar da rahoton mutuwarsu a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo bayan da wani tsohon jirgin sufurin saman Rasha na dakon kaya ya afka musu, wato kirar Ilyushin 76 na dakon kaya, wanda kai-tsaye ya afka musu ya sunkucesu ya watsar waje.

6 ga Maris: Wani jirgin saman Algeria kirar Boeing 737 ya yi hadari bayan tashinsa daga filin jirgin saman Tamanrasset, inda kimanin mutane 102 suka mutu.

19 ga Fabrairu: Wani jirgin saman soja na kasar Iran na sufuri dauke da mutane 276 ya yi hadari a kudancin kasar, inda dukacin mutanen cikinsa suka mutu.

8 ga Janairu: Wani jirgin sufurin Turkiya na Turkish Airlines A Turkish Airlines dauke da fasinjoji 76 tare da matukansa ya yi hadari yayin da yake kokarin sauka a Diyarbakir.

2002

23 ga Disamba: Wani jirgin sufuri na Antonov 140 dauke da kwararrun masana harkar hada-hadar jiragen sama ya yi hadari a tsakiyar kasar Iran, inda ya halaka daukacin mutane 46 da ke cikinsa. Tawagar masana sun yi tafiyar da zimmar nazarin yadda za su inganta irin wannan jirgin da Iran ta kera bayan da aka ba ta lasisin izinin yin hakan.

27 ga Yuli: Wani jirgin yaki ya yi hadari inda ya fada cikin taron jama'a 'yan kallon wasa da ke wani gari a Yammacin kasar Ukrain na Lviv, inda ya halaka mutane 77, al'amarin da aka yi nuni da cewa shi ne hadarin jirgin sama mafi muni a duniya.

1 ga Yuli: mutane saba'in da daya, wadanda mafi yawansu kananan yara lokacin da jirgin Rasha kirar Tupolev 154 ya yi hadari a wata tafiya da 'yan makaranta suka yi zuwa kasar Spaijn a jirgin sama kirar Boeing 757 na sufuri da ya yi karo da jirgin a kudancin Jamus.

25 ga Mayu: Jirgin swama kirar Boeing 747 mallkar kassar Taiwan na China Airlines ya yi hadari inda ya afka cikin teku kusa da tsibirin Penghu da ke kasar Taiwan, tare da fasinjoji 225 da matukansa.

7 ga Mayu: Jirgin saman kamfanin sufurin jiragen sama na China Northern Airlines plane dauke da mutane 112 ya afka cikin teku kusa Dalian a Arewa maso Gabashin kasar Sin.

7 ga Mayu: Irin wannan ranar dai, Jirgin sufurin saman kasar Masar na EgyptAir kirar Boeing 735 ya yi wata irin saukar harigido a kusa da Tunis (babban birnin Tunusiya) tare da fasinjoji 55 da matukansa mutum 10. Mafi yawan mutanen duk sun tsira daga wannan kwarya-kwaryan hadari.

4 ga Mayu: Wani jirgin sama kirar A BAC1-11-500 mallakar EAS Airlines ya yi hadari a birnin Kano da ke Najeriya, inda ya halaka mutane 148 - kimanin rabinsu hadarin ya rutsa da su ne a kasa.

15 ga Afirilu: Jirgin sufurin kasar Sin na Air China flight 129 ya yi hadari lokacin da yake kusantar Pusan da ke kasar Koriya ta Kudu, tare da da fasinjoji 160 da matukansa.

12 ga Fabraru: Wani jirgin sama kirar Tupolev 154 mallakar kamfnain sufuri na Iran Air ya yi hadari a tsaunukan Yammacin kasar Iran, inda ya halaka daukacin mutane 117 da ke cikinsa.

29 ga Janairu: Wani jirgin sama kirar Boeing 727 na kamfanin sufurin jiragen saman kasar Ecuadore na TAME Airline ya yi hadari a tsaunukan da ke kasar Colombiya, inda ya halaka mutane 92 da ke cikinsa.

2001

12 Nuwamba: Jirgin sufurin saman Amurkawa na American Airlines kirar A-300 mai zuwa Jamhuriyar Dominican ya yi hadari bayan tashinsa daga wata unguwa da ke Borough na Queens da ke New York, inda daukacin mutane 260 suka halaka, tare da wasu mutane biyar da hadarin ya rutsa da su a kasa.

8 ga Oktoba: Wani jirgin sufurin yankin Scandinavia na Scandinavian Airlines System (SAS) ya yi taho-mu-gama da wani karamin jirgin sama a yayin matsanancin hazo da ke kan titi tashin jirgin sama na filin jirgin saman Milan Linate, inda ya halaka mutane 118 da ke cikin jirgin.The crashed American Airlines flight of November 2000 left much of the Rockaway neighbourhood of New York enveloped by smoke
4 ga Oktoba: Jirgin sufurin saman Rasha na Russian Sibir Airlines kirar Tupolev 154 da ke kan hanyarsa ta zuwa Tel Aviv (babban birnin kasar Isra'ila) zuwa Novosibirsk a Siberia (wani yanki na kasar Rasha), yayin da ya raba tsaka a sararin samaniya sai ya yi bindiga ya tarwatse ya fada cikin tekun Black Sea, inda ya halaka fasinjoji 78 da matukansa.

3 ga Yuli: Jirgin saman Rasha kirar Tupolev 154 da ke kan hanyarsa ta zuwa Yekaterinburg da ke tsaunukan Ural da ke kaiwa zuwa ga tashar jiragen ruwan Rasha na Vladivostok, inda ya fada birnin Siberia a garin Irkutsk, inda fasinjoji 133 da masu kula da fasinjojin 10 suka halaka.

2000

30 ga Oktoba: Jirigin sufurin saman kasar Singapore Airlines kirar Boeing 747 da ya tashi zuwa Los Angeles ya yi hadari daga tashinsa a filin jiragen saman Taipei da ke kasar Taiwan, inda ya halaka mutane 78 daga cikin mutanen 179 da ke cikinsa.

25 ga Yuli: Jirgin saman Faransa na Air France Concorde da ke kan hanayarsa ta zuwa New York ya yi hadari inda ya fada wani Otal da ke wajen birnin Paris jim kadan da tashinsa, inda ya halaka mutane 113, wadanda suka hada da wasu mutane hudu da hadarin ya rutsa da su a kasa.


The Singapore Airlines Boeing 747 heading for Los Angeles crashed soon after take-off from Taipei airport in Taiwan
17 ga Yuli:Jirgin saman Alliance Air kirar Boeing 737-200 ya fada kan wasu gidaje yayin da yake kokarin sauka a Patna da ke kasar India, inda ya kashe mutane 51 da ke cikinsa tare da wsu mutane hudu da ke kasa.

19 ga Afirilu: Jirgin saman Air Philippines kirar Boeing 737-200 wanda ya tashi daga Manila zuwa Davao daf da saukarsa kasa ya yi hadari, inda ya halaka daukacin mutane 131 da ke cikin jirgin.

31 ga Janairu: Jirgin sufurin saman Alaska Airlines MD-83 wanda ya taso daga kasar Mexico zuwa San Francisco (na kasar Amurka) ya fada cikin teku da ke gabar Kudancin California, inda daukacin mutane 88 da ke cikin jirgin suka halaka.

30 ga Janairu: Jirgin sufurin sama na kasar Kenya mallakar Kenya Airways kirar A-310 ya fada cikin tekun Atlantic jim kadan da tasowarsa daga Abidjan da ke kasar Ivory Coast, a kan hanyarsa ta zuwa Legas a Najeriya. Daukacin mutane 179 ban da mutum 10 da ke cikin jirgin sun mutu.

1999

31 ga Oktoba: Jirgin saman sufurin kasar Masar na EgyptAir kirar Boeing 767 ya yi hadari a tekun Atlantic bayan da ya taso daga filin jiragen saman John F. Kennedy da ke New York da zimmar zuwa Cairo babban birnin kasar Masar, inda ya halaka daukacin mutane 217 da ke cikinsa.

24 ga Fabrairu: Jirgin sufuri na kamfanin China Southwest Airlines y yi hadari a gabar ruwan kasar Sin Lardin Zhejiang bayan da ya raba tsakiya a sararin samaniya sai ya yi bindiga (ya fashe). Daukacin mutane 61 da ke cikin jirgin kirar Rasha samfurin TU-154, wanda ya taso daga Chongqing zuwa Kudu masio gabashin birnin Wenzhou duk mutanen ciki sun mutu.

1998

11 ga Disamba: Jirgin sufurin kasar Thailand na Thai Airways International kirar A-310 ya yi hadari a sufurin cikin gida lokacin yunkurinsa na uku wajen suaka a Surat Thani da ke Thailand, inda ya halaka mutane 101.

2 ga Satumba: Jirgin sufurin saman kasar Switzerland na Swissair MD-11 da ya taso daga New York zuwa Geneva sai ya yi hadari a tekun Atlantic da ke gefen kasar Kanada, inda ya halaka daukacin mutane 229 da ke cikin jirgin.

16 ga Fabrairu: Jirgin saman sufuri kirar Airbus A-300 mallakar kamfanin sufuri na Taiwan's China Airlines ya yi hadari a filin jirgin sama da ke kusa da Taipei Chiang Kai-shek yayin da ya yi yunkurin suaka a yanayin hazo da ruwan sama bayan da jirgin ya taso daga Bali da ke kasar Indonesiya. Daukacin mutane 196 da ke cikinsa tare da wasu mutane bakwai da ke kasa duk sun mutu.

2 ga Fabrairu: Jirgin saman kasar Philippines na Cebu Pacific Air DC-9 ya yi hadari a tsaunukan da ke kudancin kasar Philippines, inda ya halaka daukacin mutane 104 da ke cikinsa.

No comments