Breaking News

Tattaki zuwa Dumurkul: Kauyen da aka haifi Shugaba Buhari

Tattaki zuwa Dumurkul: Kauyen da aka haifi Shugaba BuhariAllon da ke nuna kauyen Dumurkul

Kafin Juma’ar makon jiya lokacin da aka bayyana cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gina Masallacin Juma’a a mahaifarsa Dumurkul, ’yan Najeriya kadan ne suka san kauyen na Dumurkul. Kauyen Dumurkul inda aka haifi Shugaba Buhari, yana da nisan kilomita uku ne daga garin Daura da kuma nisan kilomita biyar daga Kongolom, wani gari da ke kan iyakar Najeriya da Jamhuriyyar Nijar. Sunan kauyen ya samo asali ne daga harshen Fulatanci wanda yake nufin ‘Mashekari,’  saboda galibi mazaunansa ba su wuce shekara daya.

Kauyen Fulani marar hayaniya, Dumurkul a yanzu yana da gidaje kusan 50 da mazauna kusan 600 da suke rayuwa irin ta Fulani. Gidajen suna dauke da rufin ciyawa kuma suna hade da gonakinsu yayin da ake ganin shanu da sauran dabbobi suna kiwo a filayensa.Kauyen yana da wata fitacciyar rijiya mai tarihi da magabata suka gina lokacin da suka iso garin. Tarihin wannan rijiya yana hade ne da tarihin kauyen. Iyaye da kakanni, yayin da suka iso da dabbobinsu sun yanke shawarar su gina ta domin amfaninsu da na dabbobinsu. Duk shekara sukan ziyarce ta, kuma rijiyar ta zama abar nuni da jan hankali ga makiyaya da dama.

Akwai wani tsohon labi da ke kai mutane ga kauye a baya, amma hanyar tarayya da ta nufi Kongolom wani gari da ke iyaka da Jamhuriyyar Nijar ya matso da kauyen zuwa bakin hanya inda hanyar ta raba Dumurkul a tsakiya ya zama yana gabas da yamma.
Har yanzu mazauna kauyen Dumurkul makiyaya ne da manoma. A lokacin damina sukan daure dabbobinsu su kama noma, sannan lokacin rani wadansu sukan tafi ci-rani da dabbobin kamar yadda aka saba. Sai dai akasarinsu a yanzu suna killace dabbobinsu ne a kebantattun wuraren kiwo na gargajiya

Kauyen yana da makarantar firamare da sakandare da yara suke halarta. Kuma a cikin shekara bakwai da suka gabata suna samun ruwan sha mai kyau daga wani bohul mai amfani da hasken rana da ke ba kauyen ruwa. Sai dai kuma mutanen kauyen sai sun tafi wasu garuruwa da kauyuka kafin a duba lafiyarsu saboda rashin asibiti ko dakin shan magani.

A cewar maigarin kauyen Malam Muhammadu Nazir, Sarkin Fulanin Dumurkul, kauyen ya samo sunansa ne daga ayyukan mutane da suka fara zama a cikinsa, su ne Fulani makiyaya wadanda sukan zo su zauna da shanunsu na wucin-gadi su wuce wasu wurare. Daga baya suka yanke shawarar zama a wurin dindindin, inda kalilan daga cikinsu suka wuce. Yau da gobe sai kauyen ya zama wurin zama na dindindin kuma ya ci gaba da zama haka har zuwa yau.

Nazir ya ce: “Labarin kamar yadda iyayenmu suka gaya mana shi ne mazauna kauyen asalinsu sun fito ne daga wani garin Fulani da ake kira Kurmeji, wani kauye da ke Kudu da garin Daura na yanzu, kuma yake Karamar Hukumar Sandamu. Mazauna kauyen na farko suna isowa suka gina rijiya wadda ita ce babbar abar tarihi a kauyen. Rijiyar tana samar da ruwa ga mutane da dabbobinsu, kuma ta jawo kwararowar mutane musamman makiyaya daga Masarautar Daura a wancan lokaci.”“Labarin Kurmeji an fada mana ne. Ban taba zuwa can ba ni da kaina, saboda gaba dayan rayuwata a nan ne bayan na karbi jagoranci daga iyayena. Tarihi ne da ake bayarwa daga iyaye da kakanni. Amma iyayena sun shaida mana cewa har yanzu gonakinsu suna can, kuma wadansu daga cikin danginmu har yanzu suna zaune a can,” inji shi.

Rijiyar Dumurkul mai tsohon tarihi
 

Rijiyar Dumurkul mai tsohon tarihi

Ya kara da cewa: “Wannan rijiya yanzu haka tana cikin gonar Shugaban Kasa ce. Danginmu da na Shugaban Kasa suna daga cikin wadanda suka fara zama a nan. Sai dai ba dukansu ne suka zo ba, wadansu ba su dawo ba bayan dogon lokaci. Adamu Bafallaje (mahaifin Shugaba Buhari), shi ma ya zauna a nan. Wadancan turaku hudu da suke cikin filin, nan ne kabarinsa. Ya rasu a kauyen ne saboda ya ci gaba da zama tare da wadansu ’yan uwansa wadanda gidajensu har yanzu suna nan a Dumurkul. Kusa da sabon masallacin da ya jawo mutane da dama, shi ne gidan marigayi mahaifin Shugaban Kasar, kuma sauran kewayen wurin ne gonarsa. A wannan kauye Shugaba Buhari yana da yayye na ’ya’yan ’yan uwan mahafinsa su uku da suke raye. Gidajen da suke kusa da masallacin nasu ne.”

Nazir ya kuma nuna cewa: “Gidan Malam Sule Maikanti shi ne wanda Shugaban Kasa ya taka ya je bayan an bude Masallacin Juma’ar. Ba ya da lafiya sosai don haka Shugaban Kasa ya je gaishe shi. Sauran wadanda har yanzu suke raye, su ne Alhaji Usman Katuru da Alhaji Sale da Altine.” Ya kara da cewa aiki a gonar bai taba yankewa ba“Duk shekara yana noma duk gonakin da ya gada a kauyen. A wannan kauye mun ci sa’a muna da ruwa muna samun ruwa, duk da cewa sai a wata bakwai da suka gabata muka samu wutar lantarki, muna godiya kan haka,” inji Nazir, inda ya kara da cewa babban sana’ar mutanen kauyen har yanzu shi ne noma da kiwo. “Ba mu kauce daga abin da muka iske iyaye da kakanninmu ba. Muna alfahari da su har cikin zuciyarmu. Daga gare su muke samun abin rayuwa.”

Wani dattijo kuma babban yaya ga Shugaba Buhari mai suna Malam Sule, ya yaba wa Shugaban Kasar kan samun dama ya ziyarce shi. Ya ce, “Mahaifin Buhari yana daga cikin mutanen farko da suka fara zama tare da kafa kauyen. Baya ga kiwo da noma, Dan Bafallaje babba ne kuma fitaccen maharbi wanda gidansa ke cika da nau’o’in dabbobin da ya kamo a kowane yammaci. Ya auri wata mace da ake kira Zulai, kuma ya rasu shekaru masu yawa da suka gabata. A wancan lokaci wannan wuri daji ne cike da duhu. Mahaifin Buhari sai da ya sare itatuwa da yawa domin gina gidansa da bude gonakinsa.”Malam Sule ya bayyana Shugaba Buhari da mutum mai saukin kai, wanda ba ma iyalai da danginsa kawai yake so ba har ma da “dukan mutane. Na ji dadi da ya taka a kafa zuwa wannan daki ya zauna a can. Mun tattauna muka yi wa juna addu’o’in alheri. Yanzu ba mu da yawa. Rakiya ita ce kadai ’yar uwar Shugaban Kasar da take raye, kuma tana zaune ne a Kofar Baru da ke garin Daura,” inji shi.

No comments