Wadanda suka yi nasara da wadanda suka sha kaye: Zaben Najeriya - DWGUNSAU'S BLOG

Breaking

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Saturday, 2 March 2019

Wadanda suka yi nasara da wadanda suka sha kaye: Zaben Najeriya


Zabar Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a karo na biyu bai zo wa 'yan Najeriya da dama da mamaki ba, amma an sha mamaki sosai a zabukan 'yan majalisar tarayya.

Babban abin mamaki a ciki shine faduwar wasu manyan iyayen gidan siyasa a Najeriya wadanda suke amfani da kudi domin cin zabe da kuma daukar nauyin wasu da suke so su hau kan karagar mulki.

Wasu da suka sauya sheka tsakanin manyan jam'iyyun biyu kafin zabe su ma basu ji da dadi ba a zaben.

Ga wasu daga cikin jiga-jigan 'yan siyasan da suka sha kaye a zaben da aka gudanar na 23 ga watan Fabrairun 2019:

Wadanda suka sha kaye


1. Bukola Saraki- Shugaban majalisar dattawa


Shan kayen mutum na uku wanda ya fi kowa girman matsayi a Najeriya shine abin da yafi bayar da mamaki.

Ba wai don shine shugaban majalisar dattawa ba amma shine shugaban yakin neman zaben jam'iyyar PDP.

Ba a ga maciji tsakanin Bukola Saraki da Shugaban Najeriya wanda hakan ya jawo aka bincike shi a kan zargin cin hanci.

Kotun koli ta wanke shi daga duk wasu abubuwa da ake zarginsa a watan Yulin bara, bayan wata daya da yin haka ne ya sauya sheka daga APC zuwa PDP.

Ya nemi ya koma kujerarsa ta sanata amma a matsayin mai wakiltar Kwara ta tsakiya amma dan takarar APC Ibrahim Oloriegbe ya maye gurbinsa, hakan ya kawo karshen mulkin 'iyalen Saraki' wadanda suka shafe kusan shekaru 50 suna jan ragamar siyasar Kwara.

Ana ganin cewa mutane da dama a jihar sun gaji da rashin ci gaba a jihar, inda hakan ya janwo kirkiro wata tafiya da ake kira (''O to Ge'' movement) wace take nufin '' ya isa hakanan.''

Wannan tafiyar an kirkire ta ne domin yaki da Saraki da kuma wadanda yake daurewa gindi, wannan tafiyar ta ''O to Ge'' ta yi tasiri domin kuwa sun sha kaye a zaben.

Bukola Saraki ya rasa kujerarsa ta majalisar dattawa


2. Godswill Akpabio - sanata mai wakiltar arewa maso yammacin Akwa Ibom

Godswill Akbabio yana daya daga cikin masu ruwa da tsaki a siyasar yankin dake da arzikin man fetur a Najeriya wanda har ya yi gwamna sau biyu a jihar Akwa Ibom.

Akpabio ya yi asarar kujerarsa ga dan takarar PDP Chris Ekpenyong.

An yi fama da rikici da da zarge-zarge a lokaci yakin neman zabe a jihar. Wannan matsalar ta kunno kai ne bayan ya sauya sheka jim kadan bayan rikicinsa da gwamnan jihar Emmanuel Udom wanda Akpabio ya zaba da hannunsa ya zama magajinsa a lokacin da ya sauka daga gwamna.

Wannan ya janyo Akpabioya sauya sheka zuwa APC amma a karshe wannan ya janyo faduwarsa warwas inda jam'iyyar PDP ta lashe duka kujerun jihar.3. Rabiu Kwankwaso- Uban gida a siyasar KanoRabiu Kwankwaso ya mulki jihar Kano na shekaru takwas kuma a yanzu haka Sanata ne amma duk 'yan takarar da yake goyon baya sun fadi warwas.

Kwankwaso na daga cikin jiga-jigan 'yan siyasar Najeriya da suka shahara na wannan lokacin inda yake da dumbin magoya baya musamman 'yan akidar Kwankwasiyya wadanda suke a fadin Najeriya.

Wannan ne karo na biyu da ya rasa takarar shugabancin kasa inda a 2015 daga kuma 2019 yayi yunkurin yin takara amma bai samu nasara ba.

Kwankawaso shi ma ya sauya sheka bayan ya samu matsala da daya daga cikin na kusa dashi kuma magajinsa watau Umar Ganduje.

4. Geoorge Akume- Sanata mai wakiltar arewa maso yammacin Benue


 Dan siyasar mai shekaru 65 ya mamaye fagen siyasar jihar na kusan shekaru 20.

An zabi Akume a matsayin gwamnan jihar a 1999 wanda ya shafe shekara takwas sai a 2007 ya tafi majalisar dattawa.

Tun bayan wannan lokacin ne duk wadanda ya daurewa gindi a wannan jihar a siyasance suna lashe kujerunsu amma zaben da aka gudanar a wannan karon ya kawo karshen kaka-gidan da ya yi a siyasar jihar.

Ana danganta faduwar ta sa ne da raba gari da ya yi da gwamnan jihar Samuel Ortom wanda ya taimaka ya dora shi bisa karagar mulki a 2015, da kuma matakin da ya dauka na biyayya ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari duk da rikicin da ake samu tsakanin manoma da makiyaya a wannan jihar ta Benue.


Fiye da mutum 2000 ne suka mutu a rikicin da aka samu a jihar a bara tsakanin makiyaya da manoma
Makiyaya a jihar akasarinsu Fulani ne kuma Musulmai sai kuma manoman jihar akasarinsu Kiristoci ne.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Bafillace ne kuma Musulmi inda ake zarginsa da rashin tabuka wani abin a zo a gani wajen shawo kan matsalar tsaro a wannan yankin, amma sau da dama shugaban ya sha musanta zargin da ake masa na nuna bangaranci wajen shawo kan wannan matsalar.


5. Shehu Sani- Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya


Daya daga cikin masu caccakar tsare-tsare na shugaban Najeriya Sanata Shehu Sani, ya rasa kujerarsa ga dan takarar jam'iyyar APC.

Shan kayen Shehu Sani mai shekaru 51 bai zo wa jama'a da mamaki ba sakamakon dogon rikicin dake tsakaninsa da gwamna mai ci a jihar a yanzu Nasir El-Rufai duk da a da jam'iyyarsu daya kafin suka raba gari tsakaninsu.

Dukkansu biyu sun sha rigima a kan tsare-tsare wanda hakan yake sanadiyar kawo cece-kuce musamman a shafin Twitter.

Shehu Sani wanda marubuci ne kuma dan gwagwarmayar kare hakkin dan-adam ne yana daga kadan daga cikin 'yan siyasar da suka bayyana kadarorinsu a fili.

A watan Octoban bara ne dai Shehu Sani ya bar APC inda ya koma PRP.


BANKY W- Mawaki kuma dan wasan kwaikwayoOlubankole Wellimgton, wanda aka fi sani da Banky W ya yi kokarin samun kujerar zama dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Eti-Osa a Legas.

Mawakin dan shekara 37 ya fadi zabensa amma ya yi kokarin lashe rumfuna biyu harda rumfar da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jefa kuri'arsa.

Ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa: '' Ina fatan za mu yi waiwaye a kan nasarar da muka samu a watanni uku da suka gabata, kuma hakan ya nuna irin abinda za mu yi nan da shekaru hudu. Ina fatan mun gane cewa samun nasara a wasu sassan Eti-Osa alama ce ta za mu iya samun nasara a ko ina.''

Wadanda suka yi Nasara1. Dino Melaye- sanata mai wakiltar Kogi ta yamma


Dino Melaye sanata ne da ya yi suna wajen jawo takaddama a majalisar dattawa. Shi ne sanata mai wakiltar Kogi ta yamma kuma ake wa lakabi da ''sanata mai waka,.''

Dino Melaye ya shiga matsaloli da dama inda ciki har da matsala tsakaninsa da gwamnatin jihar Kogi sai kuma rikicinsa da hukumar 'yan sanda da kuma wasu matsaloli da ya shiga masu alaka da shari'a.

Dan siyasar na jam'iyyar PDP ya jawo cece-kuce sosai sakamakon wadaka da yake yi da dukiya.

Dino mai shekaru 45 ya sha suka a kan batun yadda yake nuna isa da dukiyarsa musamman a wani bidiyon waka da aka nuna shi a ciki na wani mawakin gambara mai suna Kach.

Amma jama'a da dama na ganin sake zaben Dino na nuna matsayin karfin siyasar talakawa kuma mutanen mazabarsa sun yi tsaye duk da abubuwan kunyar da ya tafka a baya.

A baya ma jama'arsa sun yi tsaye a lokacin da abokan hamayyarsa suka yi kokarin ganin an yi masa kiranye.

2. Aishatu Binani - 'Yar takarar sanata daga Adamawa ta tsakiya


'Yar takarar mai shekaru 47 ita kadai ce 'yar majalisar dattawa mace da aka zaba daga arewacin Najeriya a wannan lokaci .

Duk da cewa ta yi takarar ne a karkashin inuwar jam'iyyar APC, lashe zabenta ya zo da mamaki ganin cewa ta fito daga bangaren Muslmai a Adamawa dake arewa maso gabas, mahaifar dan takarar shugaban kasa daga jam'iyyar PDP Atiku Abubakar.

Jam'iyyar PDP ta lashe jihar a zaben shugaban kasa amma Aishatu Binani ta bayar da mamaki inda ta kayar da dukkanin abokan karawarta maza.

Lashe zabenta zai sanyaya zukatan matan arewacin Najeriya bayan sanata daya tilo daga arewacin Najeriya Binta Garba ta rasa kujerarta wace itama daga Adamawa ta fito.

Majalisar dinkin duniya ta yi hasashen cewa Najeriya tana daga cikin kasashen dake da karancin mata a fagen siyasa.2. Kola Balogun- Dan takarar sanata a Oyo ta kudu


Lashe zaben wannan dan takarar babban abin mamaki ne, musamman ga magoya bayan jam'iyya mai mulki ta APC a kudu maso yammacin jihar.

Lashe zaben Kola Balogun ya kawo tsaiko ga gwmnan jihar Abiola Ajimobi daga shiga tarayyar gwamnoni da suke tafiya majalisar dattawa.

3. Yakubu Dogara- kakakin majalisar wakilai


Yakubu Dogara mai shekaru 51, yana daga cikin 'yan siyasar da suka sauya sheka daga jam'iyya mai mulki ta APC zuwa PDP a bara.

Jama'a da dama sun yi tunanin cewa wannan matakin da ya dauka zai iya kawo tsaiko ga Yakubu Dogara wajen sake samun nasarar lashe kujerarsa sakamakon mahaifarsa watau Bauchi tana daga cikin wuraren da Shugaba Buhari yake da yawan kuri'u.

Amma duk da haka, Dogara wanda mabiyin addinin Kirista ne kuma yana wakiltar mazabun Bogoro da Dass da Tafawa Balewa tun a 2007 ya sha da kyar wajen kayar da jam'iyya mai mulki watau APC a wannan yankin.

Da dama daga cikin jama'ar dake mazabarsa mabiyan addinin kirista ne a jihar da addinin musulunci ya fi rinjaye, kuma ya samu goyon bayan daya daga cikin Malaman Darikar Tijjaniya.

Ana ganin cewa ba zai samu nasara ba wajen samun kujerarsa ta kakakin majalisa sakamakon APC za ta zabi daya daga cikin 'yayanta a majalisar domin rike wannan mukamin.

Nasarar da Dogara ya samu ita ce ta fi jan hankalin mutane.

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad

Responsive Ads Here