Breaking News

Wadanne kalubale ne ke gaban Abdullahi Ganduje?

Wadanne kalubale ne ke gaban Abdullahi Ganduje?

Masu zaben sun kasu gida biyu ne


Ranar Lahadi ne hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC, ta sanar da Abdullahi Umar Ganduje a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kano da aka kammala ranar Asabar.

An samu tsaiko a zaben gwamnan jihar da aka gudanar ranar 9 ga watan Maris inda INEC ta ce zaben bai kammalu ba, saboda rashin sakamakon zaben wasu mazabu a kananan hukumomi 28.

Hukumar ta zabi ranar 23 ga watan Maris don karasa zaben, inda kuma daga nan ne aka tantance wanda ya samu nasara a fafatawar da Ganduje ya yi na APC ya yi da Abba Kabir Yusuf na PDP.

Wannan ya jawo ce-ce-ku-ce a jihar, musamman ma magoya bayan jami'yyar PDP.A ganinsu, sake zaben wani shiri ne na jam'iyyar APC mai mulki na yin magudi, ganin cewa jam'iyyar PDP ce ke kan gaba da tazarar kuri'u sama da 26,000.

Sai dai tambaya mafi muhimmanci a nan ita ce, ya ya mulkin Gwamna Ganduje zai kasance a karo na biyu? Kuma wadanne kalubale ne zai fuskanta?

Rarrabuwar kan al'ummar jihar
Mai sharhi kan al'amuran siyasa Malam Kabiru Saidu Sufi ya yi tsokaci kan matsalolin da ka iya tunkaro Gwamna Ganduje a Kano.

Ya ce "Shi kansa zaben ya nuna cewa masu zaben sun kasu kashi biyu, duba da cewa tazarar da ke tsakanin yawan kuri'un jam'iyyun biyu ba ta da yawa."

A cewar Sufi, "kusan masu zaben sun kasu gida biyu ne inda ko wanne ya dauki bangare guda."

"Don haka babban kalubale a yanzu shi ne ganin yadda za a jawo al'umma a hada kansu wuri guda a mulke su, ba tare da an mulki al'umma mai rarrabuwar kai ba."

KABIRU SUFIMalam Kabiru Sufi

Malam Sufi ya ce rarrabuwar kan ba wai ta shafi masu zabe ba ne kawai, har da malamai sun kasu kashi biyu, kazalika ma shugabannin al'umma.

Saboda malaman addini na da tasiri sosai a kowace al'umma. "Shi ya sa rabuwar kan ta zama babban kalubale ga Gwamna Ganduje. "

Ya ce :"Dole ya samo hanyoyin da zai jawo hankalin al'ummar jihar don ya ji dadin mulkinsa."

Harkar Tsaro


Wannan zaben ya zo da wani yanayi na rikice-rikice a Kano, inda aka rika zargin cewa akwai bangarorin da ke hayar 'yan daba don cimma wasu bukatunsu na siyasa.

"Yakin neman zaben ya bijiro da dabanci inda aka rika ganin matasa masu rike da makamai suna yi wa jama'a barazana."

"Don haka wannan na iya zama kalubale ga Gwamna Ganduje idan ba a yi wa tufkar hanci ba."

"Akwai bukatar a inganta harkar tsaro a Kano, don kuwa harkar zaben nan ta nemi ta dawo da dabanci Kano," a cewar Sufi.

Rashin daukar tsauraran matakai na iya jefa jihar cikin "wani yanayi na rashin tsaro da zaman dardar. "

Harkar IlimiA lokacin yakin neman zabe, bangaren hamayya ya yi amfani da harkar ilimi wajen kushe gwamnatin Ganduje.

A cewarsu, gwamnatin APC ba ta mayar da hankali wajen ilimi ba musamman wajen bayar da tallafi ga daliban jihar na cikin gida da na waje.

Abdullahi Umar Ganduje ne ya lashe zaben gwamna a Kano
Yadda ake saye da sayar da katin zabe a Kano
Zaben 2019: Jihohin Najeriya da za a yi gumurzu a zaben gwamna
Wasu suna ganin an samu ci baya sosai a fannin ilimi a jihar Kano, gwamnatocin baya sun taimaka wa dalibai sosai wajen ba su tallafin karatu, amma da Ganduje ya hau mulki, sai ya rage bai wa wannan shiri fifiko.

Har yanzu akwai dalibai 'yan asalin jihar Kano da gwamnatin baya ta dauki nauyin karantunsu a kasashen waje, har yanzu wasunsun suna rayuwa a kasashen da suke karatun cikin kunci, da fargaba da rashin sanin makomar karatun na su, saboda zargin da suka yi cewa gwamnatin ta yi watsi da su.

To sai dai gwamnatin ta Ganduje tana musanta wadannan zarge-zarge.

Akwai matasan da suke kafa hujja da wannan a matsayin dalilinsu na dawowa daga rakiyar gwamnatin Ganduje.

Malam Sufi ya ce "Ya kamata wannan gwamnati ta mayar da hankali wajen ganin ta biya kudaden dalibai kuma ta ci gaba da daukar nauyin karatun yara a ciki da wajen kasar."

Inganta rayuwar al'umma


Mafi yawan kuri'un da Abdullahi Ganduje ya samu sun fito ne daga karkara.

A siyasance, ba abin mamaki ba ne don gwamnan ya mayar da hankali wajen inganta rayuwar mutanen yankin karkara, kasancewar su ne suka fi bashi kuri'a musamman a zaben 2019.

A jihar Kano, akwai kauyukan da ba su da ko famfon tuka-tuka kuma ba su da wutar lantarki, wadannan na daga cikin abubuwan da mutanen kauyukan da suka zabi Ganduje za su zura ido su gani ko zai kai masu.

Sai dai su ma jama'ar cikin birnin Kano ba zai yiwu ya yi watsi da bukatunsu ba.

Akwai ayyukan magudanan ruwa da ake bukata cikin gaggawa a cikin kwaryar Kano, da kuma rashin ruwan famfo a unguwanni da dama.

Don haka samun daidaito wajen samar da ci gaba a jihar baki daya kalubale ne babba ga Gwamna Ganduje.

Mutanen da zai yi aiki da su
Duk wani kalubale da ke gaban Gwamna Ganduje ya ta'allaka ne kan mutanen da zai zaba don yin aiki da su.

Kwamishinoninsa da masu taimaka masa na musamman na daga cikin mutanen da ya kamata ya yi nazari mai zurfi kafin ya zabo su.

Ko ba komai, yanzu lokaci ne da gwamnan zai nutsu ya karasa ayyukan da ya fara kuma ya dasa sabbi da za su zamar masa shaida ko da ya bar mulki.

Wadanda zai yi aiki da su kuwa, su ne kashin bayan duk wani aiki da zai yi ko zai karasa, ba don komai ba sai don kowanne daga cikinsu yana da rawar da zai taka a gwamnatin shugaban nasu.

Ganin cewa akwai adawa mai karfi a jihar, gwamnan zai fuskanci suka sosai a wa'adinsa na biyu.

Sannan za a sa ido sosai a kan jihar Kano saboda matsayinta a arewacin Najeriya.

Abu mafi a'ala shi ne Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya toshe kunnuwansa, ya mayar da hankali kan kawo ci gaban da ya yi wa al'ummar Kano alkawari, sannan ya nuna masu cewa lallai ya cancanci mika masa akalar jihar da suka yi.

No comments