Breaking News

Zaben Gwamna: Siyasar Kano na ci gaba da jan hankali

Zaben Gwamna: Siyasar Kano na ci gaba da jan hankaliAn fafata ne tsakanin Gwamna Ganduje na APC da Abba Kabir Yusuf na PDP
Siyasar Kano na ci gaba jan hankali, saboda girman hamayya tsakanin manyan jam'iyyun siyasa guda biyu da ke yakin lashe kujerar gwamna.

Zaben ya fi jan hankali ne tsakanin jam'iyya mai mulki ta APC a jihar da kuma babbar jam'iyyar hamayya ta PDP.

Tun kafin a fara tattara sakamakon kananan hukumomi wani bangare na siyasar ta Kano ya fara murnar nasarar lashe zabe, wani abin da ake gani zai haifar da rudani a jihar.

Wakilin BBC ya ce babu wata karamar hukuma kawo yanzu da ta bayyana cewa ta kammala tattara sakamakonta gaba daya, illa a cikin garin Kano ne magoya bayan PDP suka fara fitowa kan titi suna murna.

Kano da ke da yawan kananan hukumomi 44, Sakamakon wani yanki na birnin Kano ba shi ne zai tabbatar da wanda ya ci zaben gwamna ba, sai idan an kammala tattara dukkanin sakamakon na kananan hukumomi.

Ya ce ko wasu kananan hukumomi da ke cikin kwaryar birnin Kanon inda ake murna babu wadda ta bayyana cewa ta kammala tattara sakamakon zaben na gwamnoni har ace an kai ga bayyana sakamakon.

Kuma ya ce za a iya samun tsaikun samun sakamakon wasu kananan hukumomi saboda rashin hanya mai kyau musamman irinsu Doguwa Tudun Wada da Rogo da Kiru da Tsanyawa domin ba ba ne a kawo sakamakon cikin lokaci.Yadda 'yan a daidaita sahu suka fara murna a Kano
Kuma akwai manyan kananan hukumomi masu mazabu 14 zuwa 13 wasu 10, inda za a iya daukar lokaci kafin tattara sakamakon zaben na gwamna.

Kuma zuwa yanzu babu karamar hukumar da ta sanar da cewa ta kammala hada sakamako.

Kano na cikin jihohin da ake ganin zaben gwamna a 2019, kamar mace ce mai ciki, ba a san abin da za ta haifa ba, saboda girman adawa tsakanin 'yan takara a jihohin inda da wuya a iya hasashen wanda zai iya lashe zaben na gwamna

Murnar da wasu ke yi a birnin Kano tana iya komawa ciki, idan aka fara bayyana sakamakon wasu kananan hukumomi masu yawan jama'a kamar Gwarzo da Wudil da Karaye da Gaya da sauransu.

No comments