Breaking News

Jama'a Na Bayyana Ra'ayoyin su kan kalaman Dangote

Jama'a Na Bayyana Ra'ayoyin su kan kalaman Dangote

GETTY IMAGES

Jama'a da dama na ci gaba da bayyana ra'ayoiyinsu biyo bayan wasu kalamai da attajirin da ya fi kowa arziki a nahiyar Afirka Aliko Dangote ya yi.

A wata hirarsa da ya yi da Gidauniyar Mo Ibrahim, Dangote ya bayyana cewa ya taba zuwa banki inda ya karbo dala miliyan 10 domin ya tabbatar da cewa da gaske yana da kudi.

Dangote ya bayyana cewa da ya je bankin, ya rubuta takardar karbar kudi sai ya karbi kudin lakadan sa'annan ya zuba su a bayan motarsa.

Amma ya bayyana cewa washe gari ya mayar da kudin zuwa banki domin ci gaba da ajiyarsu.

Tun bayan wannan hira, jama'a da dama na ta bayyana ra'ayoyinsu kan wannan gajeran labarin da mai kudin ya bayar.Wannan na bayyana cewa ''gani ya kori ji, wata kila Dangote a da bai yarda yana da irin wadannan kudin ba.''Wannan kuma na cewa ''me ya sa bai mallaki kulob din Arsenal ba? Wannan ne lokacin da ya kamata ya yi cinikin kulob din.''


Sai kuma wannan ya ce ''wayyo Allah, ku taimaka ku fada masa cewa kashi daya na kudin nan za su iya sauya rayuwata gaba daya.''

Sai yaushe Dangote zai sayi Arsenal?

Aliko Dangote wanda dan asalin Kano ne shi ne dan wanda ya fi ko wane bakin mutum kudi a duniya kuma babban mai kudin Afirka kamar yadda mujallar Forbes ta bayyana.

A kwanakin baya ne dai jaridar ta bayyana cewa arzikinsa ya yi kasa a jerin masu kudin duniya, amma duk da haka ta ce Dangote ne a farko a jerin masu kudin Afirka da dala biliyan 10.3.

Sai dai mujallar Forbes din ta nuna cewa matsalar kasuwa ce da kamfanin siminti na Dangote ya fuskanta ya jawo raguwar arzikinsa.No comments