Breaking News

Lamarin sace mutane a Najeriya ya tsananta

Lamarin sace mutane a Najeriya ya tsananta

Jami'an tsaro a wasu yankunan da ake fuskantar matsalar tsaro a NajeriyaMatsalar satan mutane ana garkuwa dasu kan tituna a tarayyar Najeriya sai kara muni yakeyi,musamman ma ka titin Abuja zuwa Kaduna.

Cikin yan kwanakin nan an sace mutane da yawan gaske, lamarin da yayi matukar jefa mutane cikin mummunan tashin hankali.

A wasu yankunan kasar,Gwamnatin kasar ta sanar da kawo wasu tsare-tsare don karfafa tsaro,sai dai hakan bai hana masu gudanar da irin wadanan miyagun ayuka ci gaba da kawo cikas  ga kokarin jami'an tsaro.

Muhammad Sani wakilin Rfi daga Abuja ya mayar da hankali zuwa wannan labari tareda duba mana halin da ake ciki a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Labarai Masu Alaka

No comments