Breaking News

Miji da mata da 'ya'yansu sun mutu a hadarin mota

Miji da mata da 'ya'yansu sun mutu a hadarin mota

Mutum 13 ne suka mutu a hatsarin

Akalla mutum 13 ne suka mutu wasu shida kuma suka jikkata sakamakon wani mummunan hadarin mota a kan hanyar Bauchi zuwa Gombe a ranar Lahadin nan.

Mutanen sun hadu da ajalinsu ne da misalin karfe 2:30 na yamma, yayin da wasu motoci biyu kirar Toyota da kirar Sharon suka yi taho mu gama.

Wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan jihar Bauchi DSP Kamal Datti Abubakar ya fitar ta ce mutum 13 ne a cikin Sharon din, yayin da Toyota din kuma kirar Camry ke dauke da mutum shida.

Rahotanni sun ce cikin wadanda suka mutu din har da mata da miji da 'ya'yansu biyu.

DSP Kamal ya ce wadan da suka samu raunin suna samun magani a asibitin Tafawa Balewa dake Bauchi, yayin da kuma aka ajiye gawarwakin mamatan a asibitin.


Rundunar 'yan sandan tace har zuwa almurun Lahadin nan babu cikakken bayani dangane da inda motocin suka fito da kuma inda suka nufa.

Najeriya dai na daga kasashen da aka fi samun hadarin mota a duniya, abinda ke janyo asarar rayuka masu dimbin yawa duk shekara.

A watan Disambar bara alkaluman hukumar kare hadura ta kasa tace mutum 682 ne suka mutu sakamakon hadarin mota a kasar.

Haka kuma alkaluman hukumar kididdiga ta kasar NBS sun nuna cewa daga watan Mayu zuwa Agusta na 2018 an samu hadarin mota 2,608 a fadin kasar, yayin da mutum 1,331 suka mutu a haduran.

Hukumomi dai na cewa babban abinda ke janyo hadarin shi ne gudu fiye da kima.

Sauran manya dalilan kuma sun hada da tukin ganganci, da kin kiyaye dokokin tuki da rashin tayoyi ingantattu.

Wasu bayanai sun nuna cewa adadin mutanen dake mutuwa sakamakon hadarin mota a Najeriya ya haura wadan da ke mutuwa sakamakon cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV/AIDS.

Ambulan Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa


No comments